iRashyder
LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE : 5
Assalamalaikum, previously munyi Bayani akan
abun da mutum zai fara yi kafin Ya fara makeup
shine sanin skin type dinki da yanda Zaki kula
dashi. so, yanxn ina ga lokaci yayi da zamu shiga
kasua domin siyan kayan Kwalliya
Kina Bukatar Abubua Kamar Haka:
1 ) Cleanser + Toner
2 ) Moisturiser
3 ) makeup brushes
4 ) primer
5 ) foundation
6 ) concealer
7 ) beauty blender
8 ) setting powder
9 ) contour kit
10 ) bronzer / blush
11 ) Eye pencil
12 ) brow powder
13 ) Eye shadow primer
14 ) Eye shadow
15 ) Eye liner
16 ) mascara
17 ) lip balm
18 ) lip liner
19 ) lip stick / lip gloss
20 ) spray
Wannan sune abubuwan da kike bukata Idan
Kika shiga kasua domin siyan kayan Kwalliya
amma Idan baki da hali tou ba dole sai kin siya
dukan su
Ba sai dai akwai wanda suka zama dole kamar
su:
Moisturiser, foundation, Concealer, setting
powder
, eye pencil, eye Shadow, mascara, eye liner,
lipstick, makeup brushes da beauty blender.
YANXN ZAN KAWO KO WANNE DA YANDA
ZAKI YI AMFANI DA SU
1 ) CLEANSER : wannan amfanin sa shi wanke
fuska yanda zakiyi amfani da shi kuwa *zaki tsiya
a hannunki sai ki dan sa masa ruwa kadan
sannan ki mutstsika ki shafa a fuska amma fa ba
da Soso ba! sai ki wanke saqon hancin ki da
sama wajen gashin ki da rain idon ki domin sun fi
koma boye datti a fuska. Sannan ki dauraye da
ruwa ki sa towel mai kyau ki dan riqa daddana
fuskar ki a hankali har ki gama goge ruwan (ya
kamata ki siya karamin towel musamman dan
fuskar ki kuma ki riqa wanke shi kullum saboda
bacteria yana rage yawan kurajen fuska)
TONER : shi toner yana gyara maki fuska
musamman idan fuskar taki ta kasance mai
yawan quraje , pimples, ko kuma mai kala biyu
da sauran su yanda zaki yo amfani da shi shine
bayan kin wanke fuskan ki da cleanser sai ki
samu auduga mai tsafta ki tsiyaye toner din a jiki
ki goge fuskar ki lungu da saqo har si kin ga
babu sauran dauda sannan ki qara sa wani har
sai Kinga kin goge amma audugan bai chanza
kala ba (ban ce ki je kiyi ta durza fuskar ki ba
komai a hankali zaki yi).
2) MOISTURIZER : wannan ba wai ina nufin
Moisturiser da kike amfani da shi a jiki bane a'a
ina nufin FACE MOISTURIZER na musamman
zaki saya yanda zaki yi amfani da shi kuwa *
bayan kin goge face dinki da toner zaki bari ya
bushe (banda gajin hakuri) sannan ki dakko
Moisturizer dinki ki mutstsika a hannu sannan ki
fara tafa hannun ahankali a fuskar ki ko ya ko
ina kamar kina marin kanki amma fa a hankali!
Kamar kina taba kwai haka zakiyi tayi har sai
man ya shafu (hakan da kike yi zai sa pores
dinki silk bude yanda man zai saurin yin aiki a
fuskan ki) NOTE ba ko wane mai akeyi wa haka
ba wani zaki ga an rubta ajiki cewa ki shafa in
circular motion
Lastly duk abin da zaki siya ya zama Skin type
dinki ne in dai kina son jikin ki da kwalliyar taki
tayi kyau
Sai mun hadu a NEXT EPISODE insha Allah
WomenOfJannah
0 Comments