iRashyder
LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE : 6
Assalamalaikum, last episode munyi Bayani akan
abubua da mutum ya kamata Ya mallaka game
da kayan Kwalliya sannan mun fara Bayani akan
wasu daga ciki wato CLEANSER, TONER and
MOISTURIZER tou gaskia yana da kyau ki kiyaye
yin hakan kullum da safe da kuma dare zai gyara
maki fuska sosai ki kiyayi kwanciya da makeup a
fuska.
3) MAKEUP BRUSHES :
Da yawa sun dade yana amfani da makeup
brushes ba tare da ganin amfanin su ba har ma
kina tunanin cewa hannun ki ya fi. Tou ba haka
bane matsalar shine ba masu kyau kike saya ba.
YANDA ZAKI GANE MAI KYAU SHINE idan kika je
siya tou ki dora a hannun ki idan ya durmushe
wato yana da laushi sosai tou ba mai kyau bane
amma idan kin daura kinga ya tsaya chak! Kuma
yana da laushi bai chake ki kamar tsintsiya ba
Tou shine mai kyau din.
Yanxn zan kawo kadan daga cikin makeup
brushes da yanda zakiyi amfani da su
FOUNDATION BRUSH
Wannan brush din zakiyi amfani dashi ne wurin
shafa foundation da smoothing dinsa
KABUKI BRUSH
Zakiyi amfani da shi wurin shafa bronzer / blush
wato dan sama kadan da qashin kumatun Ki
POWDER BRUSH
Zakiyi amfani da shi wurin shafa powder mai gari
bayan kin dangwali powder din sai ki dan
kakkabe kadan sannan ki shafa daga goshin ki
zua hanci da gemun ki
ANGLE BRUSH
Zakiyi amfani da shi wurin fitar da shape din
fuska wato daga saqon hancin ki zua kunne
wurin sajen ki
CONCEALER BRUSH or COMOFLAGE
Zakiyi amfani da shi wurin shafa concealer a
qasan idon ki da saqon da ke tsakanin idonki da
hanci sannan zaki iya amfani da shi wurin gyara
shape din bakin ki da concealer bayan kin shafa
jan baki.
ALL OVER EYE SHADOW BRUSH
Zaki yi amfani dashi wurin yin smoky eyes wato
dashi zakiyi amfani wurin shafa eyeshadow a
idonki ta qasa.
BLENDING BRUSH
Zaki yi amfani da shi wurin fitar da shape din
qashin idon ki ta sama (wato tsakanin idonki da
girar ki) crease .
SPONGE APPLICATOR
zaki yi amfani da shi wurin shafa eyeshadow
SMUDGER BRUSH
zaki amfani dashi wurin rage ma kwalliyan idon ki
karfi especially eyeliner
ANGLE EYELINER BRUSH
Idan eyeliner dinki bana ruwa bane wato mai
maiqo kenan tou dashi zakiyi amfani wurin lining
idonki
LASH BROW /COMB
Zaki yi amfani da shi wurin tace gashin gran ki
da gyara shi
FAN BRUSH
Wannan zaki yi amfani da shi wurin share datti a
fuskan ki a lokacin da kike kwalliya misali idan
kin sa eyeshadow burbudin sa ya zuba maki sai
kisa fan brush din ki sharce amma sama sama
kar ki danna
BEAUTY BLENDER
zakiyi amfani da wannan wurin daidaita yawan
foundation da concealer din da ke Fuskar ki
yanda zakiyi shine bayan kin gama kwalliya kafin
ki shafa powder sai ki sa beauty blender din kina
dan daddana wa a fuskan ki har sai kin ga fuskar
ki tayi sumul zaki iya sa shi a ruwa ki matse da
kyau sannan ki fara daddana wa din hakan zai sa
face dinki tayi sumul kuma makeup din zai fi
dadewa.
Lastly ki riqa yawan wanke makeup brushes dinki
saboda bacteria yin hakan zai kare fuskar ki
daga yawan kuraje da pimples. Sai mun hadu a
NEXT EPISODE insha Allah
WomenOfJannah
0 Comments