LET'S TALK ABOUT MAKEUP EPISODE : 7

Assalamu alaikum

LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE : 7
Assalamu alaikum, previously munyi Bayani akan
makeup brushes da uses dinsu sannan mun fadi
cewa a kiyaye tsabtar sa domin kare fuska daga
yawan kuraje pimples da sauran su tou yau insha
Allahu zamu cigaba.
4 ) PRIMER
Shi primer kamar foundation yake sai dai shi
bashi da kauri idan kin shafa kamar man shafawa
haka yake amfaninsa shine;
Yana riqe foundation sannan yasa kwalliyar ta
dade ba tare da ta lalace ba. Yana batar da
alamomin tsufa a fuska (wrinkles ) yana batar da
fine lines wato layin da suke fitowa a fuskar ki
bayan kin gama kwalliya musamman layin da
yake fitowa daga saqon hancin ki zua bakin Ki
idan kinyi murmushi (yana bata ado)
Sannan wasu daga ciki suna rage maikon fuska
(idan kin siya na oily skin kenan)
Sai dai yanxn salon ya chanza domin anyi prima
ne ta kaloli daban daban kuma kowane aikin sa
daban don haka ku taho kar a barmu a baya.
CLEAR PRIMER
duk abinda na lissafa a sama yana yi sai dai shi
baya boye tabo da sauran su amma zai daidaita
maki zaman foundation dinki
GREEN PRIMER
Yana batar da jajayen tabo na kuraje da pimples
in har kina da jajayen tabo ko kuraje tou wannan
zai dace dake
So idan kina da jajayen kuraje a fuskar ki gwada
wannan:
Physician’s Formula Mineral Wear Correcting
Primer in Green ko kuma Clinique Superprime
Color Corrects Redness
BRONZE / GOLD
Ya da kyau ga bakar fata da kuma fata wacce
take da duhu ba mai haske sosai ba
YELLOW PRIMER
Wannan yana da lightening effect don haka zaki
yi amfani da shi idan fatar ki tana da alamar
quna ko dabbare dabbare sannan yana boye tabo
shima wannan yafi dacewa da baqar mace da
kuma tsaka tsaki.
PURPLE PRIMER
Wannan yafi dacewa da farar fata shima yana
boye chaki chakin fuska.
PINK PRIMER
Wannan yana karawa fuska kala mai kyau sannan
yana dacewa da ko wane kalar fata zaki iya
jaraba wannan Revlon PhotoReady Colour
Correcting Primer
ORANGE PRIMER
Wannan amfanin su daya da pink amma shi yana
boye tabo ki gwada
Revlon Photo Ready Color Correcting Primer ko
kuma Clinique Super Prime Colour Corrects
Discolorations
MULTI PRIMER
Wannan ga mai son amfani nau'i daban daban na
primer sai ya siya wannan domin yana dauke da
nau'in kaloli a cikin sa sai ki lura da irin colors
din da ke ciki kafin ki saya
YANDA AKE AMFANI DA PRIMER
bayan kinyi cleansing fuskar ki kinyi toning da
moisturising sai ki jira kamar minti 5 sannan ki
shafa primer dinki shi ba'a shafa shi da makeup
brush yafi kyau ki shafa shi da hannu domin
tamkar mai yake
Amma idan na kuraje zaki shafa tou zaki shafa
ne kawai a kan kurajen.
Zamuyi Bayani akan hakan a gaba.
Masu pimples da chaki chakin fuska ku gwada
wannan.
BareMinerals bareVitamins Skin Rev-er Upper ko
kuma Smashbox Photo Finish Blemish Control
Primer
OILY SKIN
Boots No7 Beautifully Matte Makeup Base ko
kuma BareMinerals Primetime Foundation Primer
DRY SKIN
Palladio Primer ko kuma Laura Mercier Hydrating
Foundation Primer
SENSITIVE SKIN
Ulta Professional Hydro Primer ko kuma Lorac
I’m So Soothing Face Primer
Da wannan muka zo karshen wannan episode din
zamu cigaba daga Inda muka tsaya a NEXT
EPISODE insha Allah duk mai tambaya tayi a
comment box ko kuma ta private
AdoDaKwalliya

Post a Comment

0 Comments