LET'S TALK ABOUT MAKEUP EPISODE : 8

LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE : 8
Assalamu Alaikum previously muyi Bayani akan
Primer yau Zamuyi Bayani akan foundation insha
Allah
FOUNDATION
Foundation wani sinadari ne daga cikin sinadaran
kwalliya wanda yake da matsayin tushen kwalliya
(Makeup base) yana taimaka wa wajen daidaita
kalar fatan fuska ta zama daya tare da batar da
duk wani dabbare dabbare sannan shi din baya
batar da kuraje da manyan tabbai don haka mu
daina kwaba foundation a fuska please rashin iya
ado ne. Sannan tana sa fuskar ki tayi fresh (idan
baki maka da yawa ba kenan) kuma tayi sumul.
Akasarin fuska ana rufe ta ne da foundation idan
za'a yi makeup za'a shafa foundation da
foundation brush daga fuska zuwa wuya domin
kada kamanninsu su banbanta da juna.
Foundation ya kasu kala kala kamar haka
1) LIQUID FOUNDATION
Wannan zaki gansu akasari a cikin tube ko kuma
cikin kwalba mai bakin pampo basu da kauri
sosai kuma sun fi sauqin amfani suna bin fata
sosai sannan zasu sa face naki tayi sumul tayi
kyau. Shima din ya kasu kashi biyu akwai
a) OIL BASED FORMULA LIQUID FOUNDATION
Yana da kauri sannan baya mutstsikua da
sauri.Wannan shi yafi dacewa da DRY SKIN kuma
fata mai tattarewa wato WRINKLED SKIN
(alamun tsufa) sabda sinadaran dake Ciki.
b) WATER BASE FORMULA LIQUID FOUNDATION
Wannan bashi da kauri kamar oil base sannan
yana da sauqin amfani. Yafi dacewa da OILY
SKIN da NORMAL / COMBINATION SKIN domin
yana dauke da sinadarin man silicon wanda zai
taimaka wajen daidaita maiqon fuskar ki.
2) CREAM FOUNDATION
Zaki ganshi kamar cream an sa a abun jambaki
(container) amma bai da tauri sosai ko a abin
powder ko kuma tube. Shima saboda kauri sa
yana boye blemishes din fuska.
Yafi dacewa da EXRA DRY SKIN saboda
moisturising properties dinsa
3) CAKE OR STICK FOUNDATION
Zaki gana a containa kamar ta jambaki ana fito
dashi ana maidawa sannan yana da tauri sosai
fiye da wancan kuma yana saurin bushe wa idan
aka shafa a fuska sannan ya bada MATT finish
zaki iya amfani da shi a matsayin concealer (in
baki da ita) yana batar da kananan tabo amma
an fiso kiyi amfani da ita lokacin buki, dauka
hoto, ko wani sha'ani sabda qarfin ta.
Wannan foundation din tafi dacewa da OILY SKIN
sabda saurin bushewar ta Sam! Bata da maiko.
4) POWDER FOUNDATION
Zaki gansa kamar powder mai gari (loose
powder). Akwai mai kama da pressed powder
(wato powder irin mai mudubi da Soso aciki
amma ba mai gari ba) bashi da maiqo kamar
powder yake
a)LOOSE POWDER FOUNDATION
Yana dacewa da mace wacce bata cika son
kwalliya ba domin zai taimaka wajen bata
NATURAL LOOK . Sannan ana amfani da shi
wurin gyara qalliya yafi dacewa da OILY SKIN
b) PRESSED POWDER FOUNDATION
kamar yanda nayi Bayani a sama shi ba mai gari
bane kamar. Ko wane irin skin type zasu yi
amfani dashi amma yafi dacewa da oily skin
5) WATER PROOF FOUNDATION
Yana zuwa a yanayin liquid ko na cream anma
zaki ga an rubta masa waterproof ajiki. Mutane
sun fi son wannan especially lokacin zafi ko na
damuna domin shi rua ko zufa basa bata sa.
Ko wani SKIN TYPES zasu yi amfani da shi sai
da ki duba wanda aka rubta misali for dry skin ko
oily ko combination da sauran su
6) MINERAL FOUNDATION
Wannan anyi su ne da sinadaran da ake tonowa
daga qarqashin qasa kuma yafi dacewa da
SENSITIVE SKIN saboda magunguna da ya quna
8) SPRAY FOUNDATION
Zaki gansa kamar turare fesawa zaki riqa yi a
maimakon shafawa yana da matuqar kyau amma
idan kin iya fesawan idan baki iya ba ki fesa a
makeup brush dinki ki shafa ana amfani da shi
ne idan an San kwalliyar zata dade misali idan
zaki je office ko sch kuna baki sou kiyi kwalliya a
chan. All skin types akwai sai ki nemi daidai da
skin dinki
9) CREAM -TO-POWDER / LIQUID -TO-POWDER
Zaki ganshi kamar powder (compact powder) ba
mai gari ba ana shafa shi kai tsaye kamar
powder yana da maiko kadan sannan yana da
saurin bushewa yafi dacewa da COMBINATION /
NORMAL SKIN
10) TINTED MOISTURIZER
wannan Moisturiser ne da foundation a waje daya
duk da cewa wasu basu dauke sa matsayin
foundation ba shima yana gyara fuska sosai
kuma yafi dacewa da DRY SKIN.
MOUSSE /WHIPPED FOUNDATION
Zaki ganshi liquid ko cream a cikin gwangwani ko
spray sannan shi dan kadan ake shafawa
Kowane skin type zasu yi amfani da shi sai dai
yafi dacewa da DRY SKIN Da kuma TSOHUWAR
FATA kamar shakara 30
Yanda zaki gane kalar foundation dinki shine ki
shafa daga saman gemun ki zua wuyan ki idan
kika ga foundation din ta bace to kalar ki ce
amma idan kika ganta baro baro to NO! Lastly
yana da kyau mu riqa sayan kayan makeup masu
dauke da sinadarin SPF sabda kariya daga rana
bye sai mun hadu A NEXT EPISODE insha Allah
AdoDaKwalliya

Post a Comment

0 Comments