LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE : 9
Assalamu alaikum, previously munyi Bayani akan
makeup foundations da yanda ya kamata ayi
amfani da su. Yau insha Allah zamu tattauna
akan concealer.
CONCEALER
Amfani da abu mai kyau wanda ya dace da fatar
ki shine Babban abin lura a gurin kwalliya
Concealer mai kyau itace wadda take qara wa
fuska kumari ta batar da tabboi dabbare dabbare
acne da sauransu. Sannan itace wacce zata
daidaita akan foundation dinki tare da taimakawa
wajen fitar maki da even skin tone naki
AMFANIN CONCEALER
Kafin mu kai ga siya da shafa concealer yana da
kyau mu San amfaninsa da kuma muhimmancin
sa
Da farko dai ita concealer ana amfani da ita ne a
qananan wuraren da hasken su ya dashe a fuska
( kamar qasan ido, saqon hanci, tabo da acne)
sannan ba'a yi sa Don ashafa dole da foundation
ba amma yafi kyau idan aka shafa saman
foundation din.Zaki iya shafa concealer kafin ko
bayan shafa foundation amma ya danganta da
yanda kike Son boye tabban fuskar ki. Masana
kwalliya sunce idan kina da tabo sosai a fuska
yafi dacewa ki shafa concealer kafin ki dora
foundation wasu kuma suna ganin foundation yafi
dacewa a qasan concealer tou ko ma dai yaya
ne sai ki gwada duk biyun ki zabi wanda yafi
dacewa dake. Sai dai baza ki shafa concealer a
saman foundation mai kamar powder ba (ina
nufin powder or cream to powder foundation idan
baki ga post dina na foundation ba zaki iya
dubawa a Facebook page dina mai suna Ado Da
Kwalliya)
ZABAN CONCEALER
A lokacin da zaki sati concealer yana da kyau ki
dage wurin zaben wanda ya dace da fatar ki
(skin type) don haka idan dry skin Gare ki tou
kada ki sayi concealer na LIQUID KO MATTE
FINISHED domin zai sa fuskar ki ta dada
bushewa kenan yafi dacewa da oily skin domin
zai taimaka wajen rage maiqon fuskar
Amma mai Oily skin Da kuma wanda ramukan
jikin sa suke da girma (ina nufin kafan gashin
jikin ki) tou bazai amfani da CREAMY KO STICK
CONCEALER ba. Sabda zai shiga cikin ramin
gashin ya qarawa ramukan girma sannan irin
wannan concealer din suna qarawa fuskar mutum
maiko kenan yafi dacewa da dry and normal skin
amma ba masu open pores ba (kafan gashi a
bude)
Idan kuma kina da yawan tabbai a fuskar ki yana
da kyau ki sayi concealer da aka sanya masa
Medium coverage
Sannan yana da kyau ki siya concealer guda biyu
wato wanda zaki riqa shafawa a qasan idon ki da
kuma wanda zaki riqa shafawa sauran wuraren
yanda kuwa zaki banbance su shine misali
FOUNDATION. # COLOR3
CONCEALER. #COLOR3/2
UNDER EYE CONCEALER # COLOR1/2
Ana so kalar foundation dinki da concealer su
zama daya wato akwai kala mai sanyi mai dumi
da kuma mai haske (warm, cool and bright
colours) idan foundation dinki mai kalar sanyi ne
tou concealer din ma ya kasance haka.
TYPES OF CONCEALER
LIQUID CONCEALER
yafi dacewa da normal, combination, oily,
sensitive skin Da kuma fuska mai chaki chaki
sannan idan zaki sayi under eye concealer tou
yana da kyau ki sayi liquid zakiyi setting dinsa da
ko wane kalar pouda
CREAM CONCEALER
Yafi dacewa da dry skin normal skin combination
da kuma sensitive skin sannan idan kinyi amfani
da shi tou akwai buqatar ki shafa loose powder
(powder mai gari )
STICK CONCEALER
Normal, dry, da kuma sensitive skin sannan
bayan kin gama akwai bukatar kiyi setting dinsa
da powder mai gari
CREAM TO POWDER CONCEALER
Yafi dacewa da normal combination da kuma
sensitive skin wannan ba ya buqatar ki shafa
masa powder idan kin gama sannan idan kina da
acne tou zai qara maki yawan su don haka masu
pimples da dry skin ku guje sa
COLOUR CORRECTING CONCEALER :
Shi wannan ba sai nayi wani dogon Bayani ba
domin dai suna zua ne kala daban daban Kamar
da purple , pink da sauran su functions dinsu
daya da na primer masu colour dan haka idan
xaki siya concealer mai colour sai ki duba post
dina na primer dan ganin amfanin ko wane kala
Wannan sune nau'o'in concealer kuma ko wanne
daga cikin su yana da kyau Sosai abu mai
mahimmanci dai kawai ki zabi wanda yafi
dacewa da skin type dinki next episode zamu
koyi yanda ake amfani dashi insha Allah wslm.....
AdoDaKwalliya
0 Comments