MASU FAMA DA DOTTIN HAKORI, KO AMOSANIN HAKORI, DA SAURAN CUTUKAN HAKORI, GA MAGANI FISABILILLAHI,

 MASU FAMA DA DOTTIN HAKORI, KO AMOSANIN HAKORI, DA SAURAN CUTUKAN HAKORI, GA MAGANI FISABILILLAHI,


Duk wanda yake fama da dishewan hakori wato kana brush kullum amma hakorinka yaki ya yi fari, ko kana fama da warin baki, idan kaci karo da wannan rubutun kada ka yi wasa gurin gwadawa insha Allah za'a dace,


Akwai abin da yake jawo warin baki irin local factors, akwai poor oral hygiene, wato rashin kula da tsaftar baki,


1 Shan taba, 2 Kurji a cikin baki, 3 Mouth ulcer, 4 yawan cin tafarnuwa, 5 Shan giya 6 Cin goro, 7 Cin albasa, 8 Rashin cin abinci,masu fama da matsalolin cikin baki sai ku kiyaye wayannan abubuwan, idan kuna bukatar rabuwa da matsalar ku cikin lokaci kan kani insha Allahu,


GA MAGANIN YADDA ZA'A RABU DA WANNAN MATSALAR INSHA ALLAH,


NA FARKO,


A sami tafarnuwa guda daya ( 1 ) sai a bare tafarnuwan,idan aka bare tafarnuwan sai a sami gireta irin abin da mata suke amfani da shi gurin kankare kwakwa,sai a goga tafarnuwan ajiki, ko kuma a daka tafarnuwan,


NA BIYU,


Sai a sami ruwan lemon tsami a zuba kadan akan tafarnuwan da aka goga ajikin giretan,


NA UKU,


Sai a sami gishiri kadan sai a zuba a kansu,


NA HUDU,


Sai a sami makilin misali kamar oral ( B ) sai a zuba kadan a kansu,


NA KARSHE,


Sai a sami wani abu kamar misalin chokali sai a gaurayasu su hadu so sai,idan ya hadu sai a sami brush mai kyawu ana dangwalan wannan hadin ana goge baki da shi,


Za'ayi haka kullum a rana sau biyu ko sai uku,na tsawon sati biyu,insha Allah duk wanda ya yi kamar yadda na fada hakorin mutum zayyi fari tas,yin farko insha Allah za'aga chanji so sai, 


Idan akwai cutukan hakori insha Allah zasu fita,jama'a zaku iya sharing na wannan rubutun,ko kuma copies domin al'umma su amfana,


GAR GADI, Kada mutum ya hada mai yawa an fiso idan za ka yi amfani da shi ka hada iya wanda za ka yi amfani da shi na rana daya,gobe idan za ka yi ka kara hada wani sabo,hakan zai fi maka amfani yadda a ke bukata,


DAGA KARSHE,


Ina kara roqon addu'oi a gareku bisa rashin lafiyar da nake fama da shi, Allah ta'ala ka bani lafiya da kaffatanin al'umma marassa lafiya amin.






Post a Comment

0 Comments