shafin hausa
TAFARKIN TSIRA (KASHI NA DAYA)
HADISI NA DAYA
MANZON ALLAH SAW YACE:
DUK ALUMMA TA ZASU SHIGA ALJANNAH SAI
WANDA
BAYA SO !
SAI SAHABBAI SUKA CE, WAYE BAYA SO, ? SAI
ANNABI SAW YACE :
WANDA YA BINI ZAI SHIGA
ALJANNAH, WANDA KUWA YA SABA MINI, BAYA
SO.
BUKHARI YA RUWAITO.
HADISI NA BIYU
MANZON ALLAH SAW YACE, :
ALUMMA TA ZATA RARRABU GIDA SABAIN DA
BAKWAI,
DUK SUNA WUTA SAI GUDA DAYA !
SAI SAHABBAI SUKA CE WACECE GUDA
DAYAR ?
SAI YACE ITACE JAMAA, WADANDA SUKE KAN
IRIN ABINDA NAKE KAI DANI DA SAHABBAI NA.
ATTIRMIZIY
YA RUWAITO.
HADISI NA UKU
MANZONALLAH SAW YACE, :
NA BAR MUKU ABU BIYU BAZA KU BATA BA
MUTUKAR
KUNYI RIKO DA SU.
1 LITTAFIN ALLAH SWT .
2 SUNNAR ANNABI SAW.
HADISI NA HUDU
MANZON ALLAH SAW YACE,:
MAI RIKO DA SUNNA TA LOKACIN DA ALUMMA
TA SAMU
SABANI KAMAR MAI RIKO NE DA GARWASHIN
WUTA.
HADISI NA BIYAR
MANZON ALLAH SAW YACE:
KU RIKE SUNNATA DA SUNNAR KHALIFOFI NA
SHIRYAYYU.
HADISI NA SHIDA
MANZON ALLAH SAW YACE:
ADDINI NASIHANE, SAI SAHABBAI SUKA CE GA
WAYE?
SAI YACE
1 GA ALLAH SWT,
2 DA LITTAFINSA
3 DA MANZONSA
4 DA SHUWAGABANNIN MUSULMI.
5 DA KOWA DA KOWA. MUSLUM,.
HADISI NA BAKWAI
MANZON ALLAH SAW YACE:
YANA DAGA CIKIN ALAMOMIN TASHIN
ALKIYAMA ZAA
DAUKE ILMI, JAHILCI ZAI BAYYANA,
ZINA ZATA YADU, ZAA SHA GIYA, MAZA ZASUYI
KADAN MATA ZASUYI YAWA, HAR A WAYI GARI,
MATA
HAMSIN NAMIJI DAYA KE KULA DA SU.
BUKHARI YA
RUWAITO.
HADISI NA TAKWAS
MANZON ALLAH SAW YACE :
ALLAH BAYA KWACE ILMI
DAGA WADANDA SUKA SANSHI , SAI DAI YANA
KARBE ILMI TA HANYAR DAUKE MALAMAI, HAR
SAI AN WAYI
GARI BABU MALAMAI, SAI MUTANE SU RIKE
JAHILAI A
MATSAYIN MALAMAI, SUNA YI MUSU FATAWA ,
SUNA
BASU AMSA DA JAHILCI SAI SU BATA KUMA SU
BATAR
(DA ALUMMA).
KOWA YA AUNA AKIDARSA, DA IBADARSA, DA
HALAYENSA DA MUAMALARSA .
HAKA MANZON ALLAH
SAW ,YAYI SHI DA SAHABBANSA.?
ALLAH KA AKAN SUNNAR ANNABI SAW, DA
KHALIFOFINSA.
shafin hausa
0 Comments