bissimallahirrahamanirrahi
Sabin posting daga shafin hausa
_YARDA ZAKI MAGANCE DUK WANI CIWON SANYI TOILET INFECTION_
Ma'anar sa:- _TOILET INFECTION_ wata cuta ce da take samun mace da namiji, cuta ce wadda take a cikin mace da kuma gaban ta. Cuta ce wadda wani zai iya daukar ta daga wani, za'a iya daukar ta idan wata tayi fitsari a daidai wani wuri kema sai kije kiyi, za kuma ki iya daukar ta ta hanyar sharing pants da wadda take dashi. Haka kuma ana iya daukar shi a yayin saduwa (sex), mace zata iya gogawa namiji haka namijin ma zai iya gogawa mace shi.
Idan na kasa mata kashi dari tou fa 95% suna da wannan cutar. Cuta ce mai matukar wahalar magani ga wanda basu san yanda zasu magance shiba.
Tambaya anan itace:- shin me yasa mutanen da basu san miye
_TOILET INFECTION_ba? Me yasa babu shi a baya?
Nikam a gani na hakan ya faru ne a dalilin yawan inserting da matan mu na yanzu keyi, matan da basu san miye cushe-cushe a gaba ba, yanzu ne abun yayi yawa. Idan ma zakiyi inserting din sai kisan abunda zakiyi dashi. Taya zaki mayar da vigina din ki tamkar wata bola? Duk abunda kikaga dama ki zuba a ciki kuma kisa ran zaki zauna lafiya? Hakan ba mai yiwuwa bane a gani na.
_ABUBUWAN DA TOILET INFECTION YAKE HAIFARWA_
rashin gamsar wa a yayin jima'i
rashin haihuwa
rikicewar al'adah
soshe-soshen gaba a cikin mutane, har wasu su ringa k'yamar ki da abun hannun ki.
_ALAMOMIN TOILET INFECTION_
fitar farin ruwa
rikicewar al'adah
kaikayin gaba
gaba ya ringa yin zafi a yayin yin fitsari
jin tsirar gaba ba tare da dalili ba
yin fitsari guntu-guntu.
_HANYOYIN MAGANCE TOILET INFECTION_
Ki daina inserting ko wane irin magani a gaban ki, sai miski, duk wata kawa ko yar uwarki da zata baki wata shawara akan ki matsa wani abu yana karin ni'imah kar kiyi wallahi, ki bata shawara itama tayi kokarin dainawa.
ki ringa tsarki da warm water, (not too hot water dan kar ya sale ki...lol)
ki ringa inserting da miski a koda yaushe, yana warkar da wannan cutar sosai.
ki ringa shan maganin bature (tabs) saboda shi zai kashe miki na cikin.
ki jika ruwan lalle amma kar ki cika lallen da yawa, sai ki zuba zuma kadan a ciki, ki ringa shan cokali uku ko wace rana, shima zai kashe miki na cikin ki sosai. Saboda ko kinyi magani na kasan ki indai kina da na cikin tou akwai matsala, saboda ciwon yana nan.
_HANYOYIN DA ZAKI BI YAYIN MAGANCE TOILET INFECTION_
ki wanke pants din ki da ruwan zafin da kika tafasa shi da gishiri, ki shanya su a rana har sai sun bugu sosai (idan so samu ne ma duka ki yarda su ki sake wasu).
duk maganin da zaki sha ya zamana mijin kima yana sha, idan kina da kishiyoyi suma susha, saboda ko kin sha magani kin warke aikin banza ne Indai suna dashi.
ki daina kwana da pant a yayin yin maganin shi, saboda ana bukatar iska ya yawaita shigar ki.
shafin hausa
0 Comments