Assalamu alaikum barkan mu da warhaka
Hausatech takawo muku,
Dabino yana daya daga cikin 'ya'yan
itatuwa masu matukar amfani ga jikin
adam saboda irin sinadaren da ya dauke
dashi. Dabino yana girme ne a bishiya
kuma 'ya'yan na cure ne kuma ya fi son
yanayi mai zafi.
Bayan 'ya'yan dabinon sun nuna ana iya
cinsu hakan nan kokuma a cire kwallon
da
ke ciki a sarrafa su ta wasu hanyoyin don
more lagwada da amfanin da dabinon ke
dauke dashi.
Ga dai wasu fa'idoji guda shida da dabino
keyi a jikin dan adam.
Wasu fa'idoji bakwai da dabino ke yi ga
jikin
dan-adam
1) Dabino nada tasiri wajen kara kuzari
ga masu aure
Binciken masana kimiyyan sinadaren
abinci ya nuna cewa dabino yana da
matukar muhimmanci wajen kara kuzari
tsakanin ma'aurata.
Domin samun wannan fa'idar, sai mutum
ya debi dabino kamar cikin hannunsa ya
jika su cikin nonon akuya su kwana, da
safiya sai a marka dabinon tare da nonon
kuma ana iya kara zuma da cardamom.
Wannan hadin yana da mutukar amfani
wajen inganta kwanciyar aure.
2) Maganin gudawa
Dabino da ya nuna sosai yana dauke da
sinadarin potassium wanda ke da
mutukar
muhimmanci wajen magance gudawa.
Sinadarin fibre da ke cikin dabino kuma
yana taimakawa wajen magance basir da
sauran matsalolin da ke da alaka da fitar
bayan gida da gyaran ciki.
3) Lafiyar zuciya
Dabino yana da matukar amfani wajen
karawa wa zuciyar dan adam lafiya. An fi
samun fa'idan da ke cikin dabinon idan
an
tsoma shi cikin ruwa ya kwana sai a
dauko a ci da safe. Hakan yana da
matukar
amfani ga masu fama da ciwon zuciya.
Sinadarin Potassium da ke cikin dabinon
yana kare buguwar zuciya da wasu
cututuka masu kama da hakan.
4) Karin kuzari
Dabino na dauke da suga wanda basu da
ila ga jikin dan adam kamar glucose,
fructose da sucrose. Saboda hakan duk
lokacin da mutum ke jin kasala idan yaci
dabino zai samu kuzari nan take.
5) Karfafa garkuwan jiki da magance
allergy
Wani abin mamaki game da dabino shine
yadda take dauke da sinadarin sulphur
wanda ba'a cika samunsa a 'ya'yan
itatuwa
ba amma kuma yana da matukar amfani
da jikin dan adam cikinsu kuwa harda
kara karfin garkuwar jiki da magance
6) Yana taimakawa masu son mayar da
jikinsu
Dabino na dauke da suga, sinadarin
Protein da ke gina jiki da kuma vitamins.
Kilogram daya da dabino na dauke da
calories 3,000 wanda hakan sun isa jikin
dan-adam biyan bukatun ta na kwana
daya.
Idan mutum ya rame kuma yana son
mayar da kibansa, dabino na iya
taimakawa wajen gina jiki sai mutum ya
jibinci cin dabinon.
0 Comments