Hanyoyin 5 da zaka dawwamar da soyayyarka a zuciyar matarka

Aure sunnah ce ta ma’aiki sannan kuma
ya kasance buri ga dukkanin masoyya,
saboda ta hakan ne zasu nuna gwanjinsu
wajen farantawa juna.

Sai dai kash, aure a zamanin da muke ciki
ya zama tamkar wasan yara musamman a
wajen Malam Bahaushe saboda rashin
martaba shi da ba a yi.
Sau tari za ka samu da an fara zaman
soyayyar ta ke gushewa sabida ma’auratan
sun gaza wajen kiyaye wasu ginshikan
soyayya da ke karfafa kauna a zukatan
juna.

Hanyoyin 5 da Zaka dawwamar da
soyayyarka a Zuciyar matarka
Da zarar an fara samun matsaloli nan da
can kuma sai ka ga duk an fara gundurar
juna. Sai danganta ta yi tsami. Sai rashin
kyautatawa ta biyo baya, daga nan kuma
sai ka ji ko dai mijin ya furta saki, ko
kuma matar ta nemi a saketa saboda
zaman ya ki dadi.

Wadannan hanyoyi guda 5 in aka rike su
sau da kafa za su dawwamar da soyayyar
mata a zuciyar mijinta.

1. Ka zamo mai tausasa zance a wajen
matarka, kar ka zamo mafadaci.
2. Idan ka shiga gida ka shiga da sallama
domin tana korar shedan daga gida.

3. Idan tazo zata zauna ka tashi ka bata
wurin zamanka, hakan zai tausasa
zuciyarta.

4. Idan zaka bata shawara ko zaka yi mata
fada ya zamo a cikin sirri, wato alokacin
da kuke ku kadai, kada ya zamo a cikin
mutane dan yin hakan muzantawa ne.

5. Ka zama mai kyautatawa matarka,
hakan yana qara soyayya.

Post a Comment

0 Comments