/meke-hana-mata-aure-yanzu. +2348141712330
Kafin muji matakin bari muyi wata 'yar
mukaddima...... . Kuyi hakuri fa yan uwa mata
har yau dai akanku ne amma yau kam abun yan
mata kadai ya shafa banda matan aure, ko
kuma dai harda matan aure saboda harda
iyayenmu mata da yayyun 'yan matan masu
aure. .
A zamaninnan namu zaka ga cewa
yarinya takai wani lokaci wanda ya kamata ace
tayi aure amma kuma sai wasu dalilai su hana
ta. Zaka ga cewa ba wai zo mata ne samari
basa yi ba, a'a suna zo mata a matakan farko
kawai dai ji take duk basa yi mata har lokaci
yazo ya qure mata, wata ma har yanzu din suna
zo mata kawai dai ji take duk basa yi mata.
To
me ke janyo yarinya tana jin hakan?? Wasu na
iya cewa JINNUL ASHIK ne. Menene jinnul
ashik? Jinnul ashik wani aljani ne da ake kira
namijin dare a hausance wannan aljanin yana
shiga jikin mace budurwa ya hana mata yin
soyayya da namiji koda mace ta fara soyayya
da namiji sai kaga tazo taji duk bata sanshi.
Haka zata fara jin damuwa haka kawai ba
abinda ya faru gareta. Ga yawan ciwon kai da
tunani, da yawan mafarkin ana saduwa da ita
dadai sauransu. Idan kuma matar aure ce itama
sai har yayi sanadiyyar mutuwar auren saboda
irin illolin da zai dinga haifarwa tsakanin
ma'auratan. To da yawa daga cikin yan uwa
mata masu fama da irin wadannan alamomin
dana lissafo a sama ba jinnul ashik ne ke
damunsu ba, jinnul dogon buri ne ke damunsu.
Ku biyo ni sannu a hanakli zaku ji ta yadda
wadannan alamomin na jinnul dogon buri suka
yi kama da alamomin jinnul ashik (aljanin
kenan). ☛
0 Comments