*A short story* *True life story*

*Ummee mukhtar*

  *A short story*
*True life story*

         *YAFARU DA GASKE*   *4DAYS AGO*

    *19 GA WATAN RAMADAN*

   *MUTUWAR BANKWANA*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭




    Wani yaro ne wanda shekarunsa 13 kwance yake akan k'afar mahaiiyarsa wacce suke kira da inna, ta zuba hannayenta biyu a fuska tayi tagumi da alama akwai abinda ke da munta, ibraheem ne wanda yad'ora kansa a cinyarta ya juyo yana kallonta , yace inna menene meke damunki?  Nan hawaye suka zubomata ta share fuskarta tace  bakomai nan ya tashi zaune yace inna kifad'i gaskiya kode bashishshikan da ake binkine suka dameki?   tace a 'a yace tokiyi hkr insha Allah idan na girma nai kud'i zansiya miki babban gida keda babana da k'anne na zan kaiki makkah zan dibo miki masu yi miki aiki kinji inna ki dena damuwa komi ze wuce.

Nan tai murmushi tajawoshi jikinta tace ibraheem kana sona kana tausayina gakade qarami amma kanada hankali Allah yaimaka albarka yace ameen inna

Qannensane suka shigo da gudu suna wasa 'yar autarsu ce ta dubeshi tace kai kaullum kana kan qafar inna koni bana hawa sekai dariya yayi yace to ai ban hanaki hawaba .

Nan yaran suka shiga daki suna wasa

Ya qara kallon inna yace inna ki hkr kinji zamuji dadi anan gaba Insha Allah ,yace yauwa inna jiya kinsan mafarkin danayi ?    Da murmushi a fuskarta tace a a gayamin

Gyara kansa yayi kan qafarta yace inna jiya nai mafarki wai gani a wani waje me girma na zama kamar balarabe se ciye ciye nake kayan kuma ga dadin wallahi

Dariya tayi tace gidan zeyi na makwaftammu....? Yace a'a inna shifa wannan gun bangama farkonsaba bare qarshensa gurin me girma ne inna amma ina farkawa naganni anan  . Dariya takumayi tace lalle ibaraheem to baka ganni a wajenba.?    Yace inna bake awajen ni kadaine amma ingafa kuma kuna gidan kawai a zuwan kuntafi unguwane

Ai batasan sanda ta qara yin dariya ba shima dariyar yake yace inna ran yaushe aka haifeni .?  Tace juma'a

Yace kuma yau juma'a ko?  Tace eh.

Yace inna kozaki qara min yawan awaran danake siyarwa danya tinda kinga azimine kuma ina ciniki

Tace a'a wannan kwano 1 ma Allah yasa mata albarka yace da kin qaramin .

Tace a'a kai hkr yace to bari nakai niqan ko

Bayan ya dawo dg kai niqa yace zetayata aiki tace a a yaje yadanyi wasan sa da abokansa tinda tallan se anjima.

Yace shide seya tayata tace a a yace to harze fita tace niko ibraheem da gobe karkai azimin nan tinda akafara fa bakasha ko daya ba yace inna ai sena kai 30 cif tace aiko sekasha so kake kayan sallah su maka yawa ?

Yace ni daba a dinkamin bama ai wa qanne na tace bakoso yace kawai bana dokin sallar ne
Inna sena dawo tace to karka jima.

Yace to yana fita yaga abokansa zasu wanka rafi yace ina zaku sukace wanka yace sekun dawo

Sukace bazaka ba nan yai shiru kamar karyaje yace sekuma yace bazamu jimaba?

Sukace eh nan suka tafi wanka rafi

Wani qaton kududdufi ne wanda aka fara aikinsa amma sanadiyyar sace daya daga cikin turawan da suke aiki awajen se suka daste ruwan yazamana cewa ya taru waje daya nan yara suke wanka

Bayan 2day aka sako baturen bayan ambiya masu garkuwa da mutanen kudi

Suna isa suka fara wanka yazamana cewa  kowa daga shi se gajeran wando da ike ruwan ya rabu 2 susecen sukai wani 6arin yayinda ibraheem yai wani 6angaren da ban .

Nan suka gama wankan suka tafi yayinda suka manta dashi .😭


Watace tazo wucewa anan taga gawar ibraheem ta ruga da gudu taje ta fad'a agidansu .

Nan mahaiiyarsa da babansa suka rude se kuka take da gudu ta nufi kogin yayinda aka bugawa yan kwana kwana waya akazo aka fidda ibraheem daga ruwa a sanqame amma idan ka kalle shi sekaga kamar yana murmushi Allah sarki rai yayi halinsa 

Ibrahim ya mutu ran juma'a  

Yana me dauke da azimi abakinsa

Yayi mutuwar shahada acikin ruwa

Sannan yazo duniya ranar juma'a bayan sakkowa daga masallacin juma'a aka haife shi😭


Tabbas inna ta shiga tashin hankali domin shika daine a yaranta yake nuna mata soyaiya da tausayi da alqawari kala kala najin dadi daze nuna mata idan ya girma.

Yau kwana 4 da mutuwar ibraheem muna addu'a Allah yajik'ansa yasa ya huta mafarkin da yai Allah yasa yazama gaske 👏🏻



Allah yasa mucika da kyau da imani yasa mi kyakykyawan qarshe ameen.👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻😭

Post a Comment

0 Comments