Jaruma fina-finan hausa na dandalin
Kannywood, Umma Shehu, ta shirya saka
wando daya da mai yi mata bita da kulli a
masana'antar fim.
Duk da cewa bata bayyana suna wanda take
mayar ma raddi, jarumar ta bayyana cewa
baza ta damu ba idan har aka kore ta daga
Kannywood.
A sakon da ta wallafa a shafin ta na kafar
sada zumunta, tauraruwar fim ta bata boye
irin rashin mutunci da zata iya yi ga wanda
ke neman fushin ta.
Tana mai cewa " Na fika rashin mutunci
kuma ni da kake kallo bana tsoron kowa sai
Allah ".
Ga cikakken sakon da ta fitar kamar haka;
"Babu abunda yadameni dakai idan kaga
dama kasa a koreni a kannywood dan nasan
bakaine me bada daukaka ba allah ne dan
haka wallahi nafika rashin mutunci nida kake
kallona bana tsoran kowa sai allah ni ummah
Shehu nafi karfin nabaka hakuri batare da
namaka laifiba dan kasa anyi dcasting dina
saime kamanta da allah shine meyi kafin
kaima kanka ai ammaka dan haka bacire ni
yakamata ayiba korana yakamata kayi
nonsense nibazansa hoto ina fadanci ba don
babu abunda nake nema agun kowa sai gun
Allah kaje katambayi waye ummah shehu
za’agayamaka irin rashin mutuncin dazanyi
kuma idan katashi tambaya kazo unguwarmu
katambaya anan ne zakaji ainihin halin
ummah babu wanda ya isah naime fadanci
idan ina sonka Ina sonka idan bana sonka
bana sonka ni haka nake dan haka to hell
with you ".
Lamarin dai ya jawo cece-kuce tsakanin
masoyan ta masu bibiyan shafinta. Wasu sun
bada ra'ayi na tayi hakuri kar ta dauki
mataki.
Haka kuma wasu na ganin dai-dai ne idan ta
nuna ma wanda ke neman ta da mummunar
harka halin ta na rashin mutunci domin
kauce ma faruwar haka nan gaba
Daga: Pulse Nigeria
0 Comments