Hanyoyi 60 Da Zaka Dawwamar Da Soyayyar
Matarka
1. Ka zamo mai tausasa zance a gareta, kar ka
zamo mai yawan fada.
2. Idan ka shiga gida kace ‘Assalamu Alaikum’,
sallam tana korar Shedan daga gida
3. Annabi SAW yace mata kamar kayan qarau ne
saboda haka kula dasu sosai, ka tuna akwai
alkhairi a cikinsu saboda haka sai a tarairayesu.
4. Idan zaka bata shawara ko zaka yi mata fada
ya zamo a cikin sirri, wato alokacin da kuke ku
kadai, kada ya zamo a cikin mutane dan yin
hakan muzantawa ne.
5. Ka zama mai kyautatawa matarka, hakan yana
qara soyayya
6. Idan tazo zata zauna ka tashi ka bata wurin
zamanka, hakan zai tausasa zuciyarta.
7. Ka guji yin fushi ta hanyar riqe al’wala a koda
yaushe. Annabin Rahma SAW yace idan kayi
fushi to idan a tsaye kake sai ka zauna, idan a
zaune kake sai ka kwanta.
8. Ka rinqa yin ado kana sa turare saboda ita.
9. Karka zamo mai tauri, Annabi SAW yace :
‘Nine mafi kyautatawa zuwa ga iyalina’, idan kayi
tauri da yawa baza ka samu kusanci zuwa ga
Allah ba, haka kuma baza ka zamo namiji jarumi
ba.
10. Ka dinga sauraron duk abinda matarka zata
gaya maka koda kana ganin abin bashi da
muhimmanci, hakan zai sa ta san ka damu da
ita.
11. Ka kaucewa cin musu da matarka, yana kawo
rabuwar kai.
12. Annabi SAW yace ku kira matanku da sunaye
masu dadi, sunan da suke so suji ka kira su
dashi.
13. Ka riqa yi mata tsarabar bazata, idan tana
sha’awar wani abin marmari sai ka sayo mata ba
tare da ta sani ba.
14. Ka kula da harshenka zuwa gareta, wato ka
guji abubuwan da zasu sa ta fushi.
15. Mutum tara yake bai cika goma ba, kayi
haquri da duk wani aibun da take dashi sai Allah
SWT ya sa albarka a cikin auren naka.
16. Ka dinga nuna mata yabo da godiya idan tayi
maka abu mai kyau.
17. Ka dinga taimaka mata wajen ganin ta kula
da dangantakar ‘yan’uwanta da iyayenta.
18. Ka yawaita janta da hira akan abinda take
so.
19. Idan kaga ‘yan’uwanta suna kusa, ka dinga
yabonta, kana kambamata, kana tabbatar musu
da kirkinta da kyautatawarta.
20. Ku dinga yiwa junanku kyaututtuka. Manzon
Allah SAW yace kyauta tana qara soyayya.
21. Idan kayi mata laifi sai ka samu wani abu ka
kyautata mata dashi dan ya goge laifin.
22. Ka rinqa kyautata zato a gareta, banda zargi!
23. Karka dinga kulawa da qananan laifukanta,
kayi kamar baka gani/ji ba. Yana daga cikin
‘dabi’un Sayyidina Aliyyu (RA).
24. Ka nin-ninka haqurinka da ita musamman a
lokacin da take jinin al’ada.
25. Ka ringa sauraron zuwan kishinta, kuma ka
ringa yabon kishin nata, ko manta Manzon Allah
SAW suna kishi!
26. Ka zamo mai qasqantar da kai, idan ka zamo
mai tunani to ka tuna cewa tana kula da
‘ya’yanka, itace mai kula da gida!
27. Karka dauki abokanka sama da matarka!
28. Ka ringa taimaka mata da ayyukan gida.
Manzon Allah SAW ya kasance yana taimakon
matansa.
29. Ka taimaka mata wajen girmama iyayenka,
baza ka iya takura mata taso su ba amma zaka
iya taimaka mata dan ta cimma hakan.
30. Ka dinga nuna mata cewa itace irin matar da
kake ta addu’ar ka samu.
31. Karinga tunawa da matarka a cikin
addu’o’inka, hakan zai qara qarfin soyayyar taku.
32. Kada ka dinga tunawa da baya, babu abinda
hakan zai jawo sai damuwa, abinda ya riga ya
wuce a barwa Allah.
33. Karka taba nuna mata cewa taimaka mata
kake idan kana mata wani abin kamar sayan
abincin gida, saboda a zahirin gaskiya mu ‘yan
aikatarwa ne kawai, Allah shine yake azurtawa da
ciyarwa. Wannan kuma wata hanya ce ta
qasqantar da kai ga Allah SWT da kuma gode
masa.
34. Ka gane cewa Shaidan maqiyinka ne amma
ba matarka ba, wani lokaci idan mata da miji
suna magana idan suka samu sabani sai Shaidan
ya shiga tsakani. Kayi iya qoqarinka wajen ganin
Shaidan bai shiga tsakaninka da matarka ba.
35. Ka ringa bata abinci a baki, Annabin tsira
SAW ya koya mana hakan, abincin ba wai iya
cikinta zai tafi ba idan ka bata a baki, har zuwa
cikin zuciyarta.
36. Ka kare matarka daga duk wani sharri ta
hanyar yi mata addu’o’in neman tsari.
37. Ka zamo mai yawan yi mata murmushi.
38. Ka guji duk abinda bata so ko mai
qanqantarsa, idan baka kula ba ta haka ne zai
girma har ya zama babba.
39. Ka guji yin fushi da fada a gareta, yin hakan
yana rage shaquwa.
40. Ka dinga yin maraba da shawarta.
41. Ka taimaka mata wajen samun nasara a
harkokinta na rayuwa.
42. Kullum ka zamo mai qara kusantuwa zuwa
gareta.
43. Ka taimaka mata wajen kula da yara. Wasu
mazan suna ganin kamar ba aikin su bane kula
da yara, basu san cewa yin hakan ne ma zai sa
su qara kima da daraja a idon matan da yaran
ba.
44. Ka ringa yi mata dadin baki da magana mai
taushi.
45. Ka ringa cin abinci tare da ita.
46. Duk lokacin da zaka yi tafiya ka sanar da ita,
haka kuma ka gaya mata rana da lokacin da zaka
dawo.
47. Kada ka fita daga gida a lokacin da kuka
samu sabani.
48. Gida yana da sirri kala-kala, idan ka zamo
mai fadan sirrin gidanka a cikin mutane to kana
yi wa kanka zaqon qasa ne. Sirrin gida ya tsaya
a cikin gida.
49. Ku dinga qarfafawa junanku wajen yin ibada,
ku dinga shirya zuwa Hajji ko Umrah a lokacin da
kowa bai takura ba (misali a lokacin da bata da
ciki kuma bata shayarwa) idan Allah ya baku iko.
50. Ka kula da haqqoqinta na aure
51. Allah SWT yace : « ku zauna da matanku
cikin kyautatawa », ka dinga riritata kamar qwai.
52. Idan aka zo kwanciyar aure kada kayi mata
‘hawan qawara’, kuyi wasan tayar da sha’awa
tukuna.
53. Idan kun samu sabani da matarka, kada ka
gayawa kowa, idan kayi haka kamar kabar ciwo
ne a bude quda ya hau.
54. Ka nunawa matarka cewa ka damu da
lafiyarta. Lafiyar matarka lafiyarka ce. Idan ka
kula da lafiyarta hakan ya nuna kana sonta.
55. Karka dinga tunanin ko yaushe kana da
gaskiya, mutum tara yake bai cika goma ba.
56. Ka ringa sanar da ita lokacin da kake cikin
matsala, farin ciki ko damuwa.
57. Ka dinga yafe mata idan tayi ba dai dai ba.
58. Kake yawan tuna cewa kaine bango wajen
jinginarta a lokutan wahala ko qa-qa nakayi
59. Ka karbi matarka da duk halin da take tashi,
Mazon Allah SAW yace an hallicci mata ne daga
qashin qirji tanqwararre, idan kayi qoqarin ka
tayar dashi zai karye!
60. Ka zamo mai kyakykyawan zato ga matarka a
koda yaushe, Allah yana kula da niyyarka zuwa
gareta a koda yaushe. Allah madaukaki yace:
“Kuma daga ayoyinsa ne cewa ya halitta muku
matanku daga gareku, kuma ya sanya qauna da
tausayi a tsakaninku, haqiqa a cikin wannan
akwai ayoyi ga masu zurfin tunani” (Q. Rum 21)
Ya Allah ka bamu abokan zama nagari, masu
tsoronka da yi maka da’a, kuma masu kyawun
gani.
0 Comments