MAFARIN SO♡♡

♡♡MAFARIN SO♡♡
♡♡♡♡♡♡♡♡
♡♡♡♡♡
1-5
©Rabiatu sk mashi
®NWA
Rerbeeart_sk @wattpad
www.babymsh.blogspot.com
Tafiya take cikin nutsuwa, burgewa, da
takun Isa, Sanye take cikin doguwan rigan
material, kalan brown da milk, saita yafa
k'aramin mayafi akai, tana rik'e da wasu
littafai a hannunta.
Bata ankara ba sai dai taji abu ya dakar
mata goshi harta kusa faɗuwa, kafin ta ɗago
kanta kawai taji an kwashe da dariya, cikin
k'unar zuciya ta ɗago da kanta tana k'arema
wurin kallo, gaba ɗaya cike wurin yake da
ɗaliban jami'ar kuma kusan duka hankalinsu
na akanta. Dariyarshi tafi shigar mata kunne,
juyawa tayi ta watsa mishi harara.
Dariya yayi irinta gogaggun en iskannan,
"zo mana" ya kirata da hannu, yana zaune
saman motah da en korenshi zagaye dashi,
taso ace zata iya komawa ta sauke mishi
duk masifan dake ranta, anma jin kanta da
tak'ama bazai taɓa barinta ba, kuma shi bai
kai ajin da zata tsaya gaban mutane tana
maida magana dashi ba. Juyawanta kawai
tayi taci gaba da tafiyanta,
Batasan sanda ya diro daga saman motan
ba, sai dai kawai taji yana neman rik'o
hannunta, cikin zafin nama ta juyo ta
wankeshi da marin da yazo mishi a bazata,
ɗaga kanshi yayi yana kallon mutanen da
sukayi cincirindo suna kallonsu, sannan
kowa ya fara k'ok'arin riƙe dariyanshi don
babu wanda baisan halin Abdallah ba.
"Ni kika mara?"
"an mareka ɗin, wannan shine gargaɗin
dazan maka na ƙarshe akan shiga harkata da
kake"
"ke kinsan waye Abdallah, wallahi sai kinyi
dana sanin marina da kikai"
"Anma bakasan wacece Rabi'ah ba, kuma
ina mai baka shawaran karka zaƙe akan
saika sani ɗin"
Nunata yayi da ɗan yasha, "zan ramane a
inda zaifi miki ciwo, kuma ki sani ban taɓa
son abu na rasa ba, ko bakiso dole kiyi
soyayya dani"
Tofar da yawu tayi a k'asa, "Allah ya
kiyayemun soyayya da ɗan shaye-shaye" ta
juya ta barshi wurin a tsaye yana huci yama
kasa maida mata magana, ya watsa ma
mutanen wurin kallo ba shiri kowa ya ɓace,
ya shige motanshi ya jata a guje.
Hankalinta kwance ta gama lecturenta suka
fito tare da Aminiyarta Amrah, hannunta taja
suka koma gefe,
"Faɗamin Rabi'ah meye gaskiyar abinda naji
wai kin mari Abdallah"
"toh meye naga duk kin wani ruɗe kaman
wani babban abune ya faru?"
"haba Rabi'ah, naga hankalinki kwance
kaman bakisan halin Abdallah ba"
"ni mamaki kike bani wallahi, siyasa ne
kawai zai nunamun, anma kuɗi kam har ke
kinsan Yayana yafi mahaifinshi sosae, don
haka duk abunda zaiyi nima zan iya, ban
taɓayin abunda nayi dana sani ba"
"hakane fa, anma ni dai duk a tsorace nake"
"kinma warware,"
Tun daga bakin gate, ma'aikatan gidan ke
kawo mishi gaisuwa anma ko kallo basu
isheshi ba, ganin motoci da yawa ya
tabbatar mishi Daddyn nashi na a ciki, don
haka kai tsaye falon Mai girma mataimakin
Governor ya wuce,
Zaune yake yana amsa waya, bodyguards
nashi zagaye dashi, yana ganin yanayin da
Abdallah ya shigo dashi, ba tare da yaa
gama ba ya katse wayan.
"Yadai Son?" cikin sham ƙamshi ya kalli
bodyguards ɗin, sannan ya maida kallonshi
kan Dad din nashi, alama ya musu da su fito,
cikin bin Umarni duk suka fita.
"waye kuma ya taɓomin kai?"
Saida ya ƙara ɓata fuska sannan ya fara
magana, "Haba Dad! Ni bansan me yasa
baka damu da abinda nakeso ba, ba ruwanka
dani sai harkan siyasarka kawai"
"akwai abinda ka taɓa nuna kanaso banyi
maka bane?"
"A'ah kawai dai wannan ne nake tunanin
bazan samu ba"
"babushi, indai Kuɗi da Mulki na iyayin komai
a duniya babu abinda zaka nema bazanyi
maka ba"
"I know Dad, but uh should promise me"
"promise"
"thank you Dad, i love you"
Sannan ya fara fara'a, jinsa yake wasai
kaman yama riga da yaa rama abinda
Rabi'ah ta mishi.
Follow me On wattpad @Rerbeeart_sk
©Rabiatu sk msh

Post a Comment

0 Comments