Mu Koyi Soyayya

💖💛 MU KOYI SOYAYYA 💞💜
A ina ake amfani da kalaman soyayya? 💖
yawancin mutane musamman samari sukan
yimin tambayoyi kamar haka:
1. Wadanne kalaman soyayya ne zan ringa
fadawa mace ta soni? 💛💞
2. Kana da kalaman soyayya masu zafi? ❤💚
3. Wadanne kalamai ne mata suka fi so? 💕
💝 da sauran su
Amsa anan shine babu wani kalamai mai zafi da
zaka fadawa mace ta soka saboda shi, 💗
hasali ma ai ba ko yaushe ake fadawa mace
kalaman ba. Dadin dadawa kuma kalaman
soyayya basu cika amfani a sabuwar soyayya
wacce bata dade ba, 💞💖💛 sun fi amfani
a soyayyar da ta riga tayi nisa, misali anan shine
ace saurayi yaga budurwa yana so sai yaje ya
fara gaya mata : Assalamu alaiki ya tauraruwar
taurari, 💚💕💘 tun daga nesa na hango
hasken walqiya da annurin fuskar ki mai kama da
farin wata daren sha uku, a gaskiya na kamu da
dimbin gigitacciyar soyayyar ki 💖💛tun dana
hango ki zuciyata ta sallama miki jiki da ruhi na,
duk duniyar nan... " haba mallam?! Indai mace
mai hankali da tunani ce daka ganin ta har ka
shiga cikin kogin soyayyar ta kayi nisa haka, 💝
💖 bayan baka san wacece itama, baka san
yaya halinta yake ba, baka san ko mutuniyar kirki
bace ko a'a ba, tasan ba ita tafi kowa kyau a
duniya ba.. Tasan cewa qarya kake dadin baki
kake mata, 💚💕💛 domin ta soka!!! Daga
farkon soyayya zuwa kafin tayi nisa babu wani
kalami mafi tasiri da zaka dinga fadawa mace ka
sace zuciyar ta wanda ya wuce ka dinga fada
mata gaskiya, 💓💞 komai zaka fada mata ka
fadi gaskiya kar ka sake ka mata qarya! Abu na
biyu kuma shine sai ka dinga fada mata irin
yadda kake sonta (misali: ina sanki har cikin
zuciya ta) ; kada ka wuce gona da iri (misali: ina
sanki tun daga cikin jijiyoyin jinin jiki da
dukkan...) ba yanzu ake buqatar wadannan ba!
Sai kuma ka dinga fada mata yadda kake tunawa
da ita idan bakwa tare, 💕💖💛 ko idan kaje
kwanciya da sauran su, amma kada ka dinga
cewa wai ka kasa cin abinci saboda tunanin ta
(ashe zaka mutu da yunwa kuwa) haka zaka ta
rainon soyayyar ta har sai tayi qarfi,
Kalaman soyayya lokacin da soyayya ta riga tayi
qarfi, bayan kun amince da halayen juna kun
yarda da kuyi soyayya, to daga nan ne zaka iya
fara amfani da kalaman soyayya duk yadda kaga
dama 💖💛💝 koda ma abinda ka fada ba
zai yuwu ba a gaske, to dai tasan cewa kana
sonta da gaskiya, 💖 hakan nema zai sa ta
qara sanin irin girman soyayyar da kake mata,
itama sai ta qara sonka.
A taqaice dai ana amfani da kalaman soyayya ne
a soyayyar da ta riga tayi nisa bayan an gina ta
akan gaskiya 💖💛💕
Aikawa da saqonnin kalaman soyayya ta wayar
salula (text message) yana da matuqar
muhimmanci a soyayya kasancewa masoyin ko
masoyiyar zata dinga dubawa a duk lokacin da
taji nishadi, 💞💗😁 ba kamar na magana
ba wanda da an fada ya wuce! Hmn, kun san me
na aikawa da Masoyiyata dazu? Cewa nayi :
"sarauniyar birnin zuciya ta a duk lokacin dana
rufe idona sai na hango ki sanye da wasu
ma'abocin korayen ganyayyaki

Post a Comment

0 Comments