KAMAR HAKA!
Na dade ina kallon taurarin samaniya
yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina
naga bakowa bace nike ganiba sai ke
masoyiyata!
So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo
jinin jikina!
Kinfita daban a cikin mata, duk lokacin da
na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar
wace sai ke!
Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu
wata a zuciyata sai ke kadai!
Yarda da amincewarki gareni, sune zasu
tabbatar da soyayyarki tagaskiya a gareni!
Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare
da bakin ciki, dan haka kowane hali nike
bazan ta6a mantawa dake ba masoyiyata!
Nakan raba dare ina mai roqon Allah don
neman biyan buqata, ko kinsan kece abu na
farko da nike roqo samu!
Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura,
tare da lullu6a da qaton mayafi amma ni duk
sanyin da ake idan na tunaki sai naji tamkar
yanayin zafi!
Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa
a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki
ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai
nayi farin ciki, idan naji tattausan muryarki,
sai nishadi da walwala tare da annashuwa
gami da farin ciki su mamaye zuciyata!
Abokina ahakan zaka bi don sace zuciyar
masoyiyarka cikin sauki!!
Kema zaki iya juya turn na wannan kalaman
domin sace zuciyar masoyinki cikin sauki!!
In kuma kinyi musu ku jaraba kugani!!
0 Comments