Wata 'yar kwalisa a Najeriya taje anyi
mata tiyatar kara girman mazaunai
- Tiyatar ta lakume mata Naira miliyan 3
- Yanzu haka dai tace kugun ta da baya na
mata ciwo sosai
Fitattar 'yar kwalisa a Najeriya mai
suna Precious Chidinma Ogbulu ta yi
bayani bayan da tayi tiyatar karin
mazaunai a 'yan watannin da suka
gabata bayan ta biya zunzurutun kudi
har Naira miliyan 3.
Kwalliya ta zo da gardama bayan da ciwo ya
kama wata budurwa da aka karawa mazaunai a
Najeriya
Sai dai Precious dake karin bayani ta
bayyana cewa har yanzu bayan ta da
kugu suna yi mata ciwo tun bayan da
akayi mata tiyatar domin ta kara kyau
a idon duniya.
NAIJ.com dai ta samu cewa mata da
yawa kan shiga halin kaka-nika-yi
musamman saboda ganin sun burge
al'umma ko kuma maza inda sukan jefa
rayuwar su cikin matsala babba.
Sai dai kuma ita Precious din tace taji
dadi da aka yi mata tiyatar domin
yanzu zata kara kyau kuma surar ta za
ta fito sosai ba kamar da ba.
0 Comments