Kamar yadda shfin jaridar The Nation ya
ruwaito mun samu rahoton cewa, kimanin
mutane hudu ne suka shiga hannun
hukuma bisa laifin yiwa kamfanin nan na
sadarwa na MTN ɓarna a yankin Mowo na
unguwar Badagry a jihar Legas.
Wannan mutane masu tayar da zaune
tsaye sun hadar da, Monday Ogbonna,
Bamiji Akanni, Sunday Odewale da
kuma Anthony Ivie da sun aikata
ta'asar ne a ranar 17 ga watan Yuli
kamar yadda rahotanni suka zayyana.
NAIJ.com ta fahimci cewa, wannan
maɓarnata sun yi amfani da wata Mota
kirar Mazda mai lambar MUS 175 XW
wajen yashe kayan aiki masu tabbatar
da ingancin sadarwa na kamfanin MTN
dake yankin Mowo.
Mutane 4 sun shiga hannu da laifin yiwa
kamfanin MTN ɓarna
An cafke wannan mutane masu son
banza a unguwar Oshodi ta jihar Legas
kamar yadda kwamishinan 'yan sanda
Imohimi Edgal ya bayyana.
Edgal ya bayyana cewa, wannan
miyagun mutane sun yi awon gaba ne
da wasu muhimman kayan aiki na
sadarwar zamani masu tabbatar da
ingancin ta masu ga masu amfani da
wayoyin salula da sauran kayayyaki
masu amfani da fasahar zamani
makamacin ta.
Ya kara da cewa, a halin yanzu dai an ci
gaba da gudanar da bincike inda za a
gurfanar dasu gaban kuliya domin
zartar masu da hukuncin da ya dace da
su.
Source:- Hausa.naija.ng
0 Comments