Mata da dama musamman ma wadanda za su yi
aure sukan biya kudi da dama domin ayi musu
kwalliyar fuska.
Wasu su kan kashe naira dubu
ashirin wasu kuma dubu goma don su samu
suyi irin wadannan kwalliya.
Ba shakka daga anga wanda akayi wa wannan
kwalliya lallai za a ce kwalliya ta biya kudin
sabulu.
Ina so na sanar da ku cewa wadannan kwalliyar
za a iya yinsu a gida idan akwai kayan aiki.
• Da farko dai ana so a wanke fuskar da sabulu
sannan a jira ya bushe kamin a shafa mata
komai.
• Ana so a sami ruwan goge fuska (cleanser) a
goge fuskar da shi da auduga.
• Bayan anyi hakan, sai a shafa man SPF (sun
protection fuemula).
• A sami hodar fandesho dai-dai kalar fatar
mutum sannan a shafa.
• A sami hoda haka a sake shafawa.
• Sannan sai a sami reza ga wanda keda cikan
gira sai a askesu kadan.
• A sami gazal din mac guda biyu; daya baki
daya kuma ba baki sosai ba sannan a zana
giran da shi.
• Bayan haka sai a sami ‘concealer’ da na ‘eye
shadow’ da brush din ‘eco tools’ da brush din
‘eyeliner’.
• Sai a fara taje giran da brush din ‘eyeliner’
• Sannan sai a zana giran da gazal din mac da
dayan mara baki sosai a hadasu.
• Bayan an shafa sai a sake tajesu da ‘eyeliner
brush’ din.
• Sai a dauko ‘brush sigma E65’ a debi eye
shadow mai duhu a sake shafawa a giran.
• A sake dauko gazal din a sake zana giran
sama da kasa.
• A shafa ‘concealer’ din da ‘brush E65’ din dai-
dai kalar fatar mutum.
• Sannan sai a shafa ‘eye shadow’ kalar kayan
da za a saka.
• Sai a shafa jan baki.
0 Comments