2019: Tsohon Gwamnan Jigawa ya nemi Jonathan ya tofa masa albarka

Idan har Sule Lamido ya zama
Shugaban kasa; zai hada kan
'Yan Najeriya – Jonathan

- Dr. Jonathan na sa rai Jam’iyyar PDP ta
lashe zaben 2019 a Najeriya

- Goodluck Jonathan yace Sule Lamido ya
cancanci mulkin kasar nan
Jonathan ya yabawa aikin da Sule Lamido yayi
a baya
Tsohon Shugaban kasa Goodluck
Jonathan ya gana da daya daga cikin
‘Yan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar
PDP Sule Lamido a gidan sa da ke Garin
Yenagoa a Bayelsa. Jonathan ya kuwa
yabawa tsohon Gwamnan na Jigawa.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa
tsohon Shugaban na Najeriya ya gana
da kwamitin yakin neman zaben Sule
Lamido jiya a gidan sa inda yace ba
shakka idan Sule ya samu tikitin PDP na
2019 zai gyara Najeriya domin kuwa ya
san aiki.

Goodluck Jonathan wanda ya ke sa rai
PDP za ta lashe zaben 2019 yace Sule
Lamido zai hada kan ‘Yan Najeriya idan
ya samu mulki.

A cewar Jonathan, kan
mutanen Najeriya ya rabu matuka a
wannan lokaci na da Shugaba Buhari
yake mulki.

Jonathan yace a 2011 lokacin da yake yi
wa kowane Gwamnan Arewa wahala ya
soki Buhari, Sule Lamido ya kan jajirce
a kan bakan sa.

Tsohon Shugaban kasar
yace Sule Lamido ‘Dan siyasa ne mai
akida kuma wanda ya san tarihin kasa.

Tsohon Gwamnan ya dai bayyanawa
Goodluck Jonathan cewa yana da
Muradin tsayawa takarar Shugaban
kasa a 2019 a karkashin Jam’iyyar
adawa ta PDP inda ya kuma godewa
irin tarbar da tsohon Shugaban kasar
yayi masa a Garin sa.

Post a Comment

0 Comments