Fatima Abdullahi Washa kamar yadda
asalin sunan ta yake ba bakuwa bace a
harkar fim din Hausa don kuwa ta fito a
fina-finai da dama inda tayi fice Duniya ta
san ta
Jarumar tana daya daga cikin manayna jarumai
mata da tauraron su ke haskawa a farfajiyar
Kannywood.
An haife ta ranar 21 na watan Febreru na
shekarar 1993.
Kwarerwar da kuma himma da take badawa a
wajen aikin yasa tayi fice cikin yan matan
Kannywood.
Wasu daga cikin tsoffin fina-finanta akwai Sarki,
'Yar Tasha, Ana Wata ga Wata, Mijin Biza, Hindu,
Dangin miji, Matar Wani da, Gwaska returns
sauransu.
Fatima ba ruwanta da fada da kowa domin
tunda take ba'a taba jinta da wani ko wata ba
suna rigima ko kuma jan fada.
Kyakkyawar jaruma har yanzu bata yi aure ba
amma akwai jita-jita da yadu shekarun baya
cewa wasu daga cikin masana'antar Kannywood
na neman ta da aure.
Daya daga cikin Nuhu Abdullahi ya bayyana
cewa hakika yana son ta kuma zai so ta zama
matar sa sai dai bai shirya yin aure ba.
Yace jarumar tana nuna masa biyayya kuma ta
taimaka mashi sosai don haka yake matukar
girmama ta.
Akwai jita-jita da take yawo akan Jarumar tana
soyayya da jarumi Adam A Zango, duk dai basu
fito fili sun tabbatar ko karyata hakan ba, Amma
kowa ya yadda fati washa tafi kowace jaruma
kusa da Adam A Zango domin tun daga fim din
'Sarki' har yanzu suna tare.
Tana kuma cikin fitattun jarumai dake da dinbim
masoya masu binta a dandalin sadarwar zamani.
Tana da mabiya dubu shida da casa'in da daya a
shafin ta na Instagram kana mabiyanta dubu
saba'in da daya ne a Tuwita.
Jarumar ta samu lamban yabon da dama cikin
gida har da wajen gida. Cikin jerin kyautar
girmamawa da ta karba akwai City people
awards.
0 Comments