AMFANIN LALLE GA MATA

Asslamu alaikum un ya kk ya gida

AMFANIN LALLE GA MATA
.
.
Lalle dai da farko wani sinadari ne mai dauke da
alfanu iri iri, kuma addini ya kwadaitar da mata
su yi lalle akwai sirrika acikin sa.
.
.
Nafarko dai lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce
daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga
cututtuka da dama, yin lalle a kafa na zuqe cutar
dake kafan sannan yana kula da dumin mace, bi
ma ana yana kiyaye. ni imar mace ba tare da ya
gushe ba, innace lalle wasu zasu dauka zanen
henna nake nufi ko, to lalle dai na gargajiya
wanda muka rabu da yinsa yanzu shi nake
magana akai:
.
.
.
Ga kuma sadaqa ga duk mai infection ta tafasa
lalle inyadan huce sai ki dinga zama a ciki na
sati biyu, in Allah yayarda za ki warke.
.
: Saboda maganin da lalle keyi ma akan iya shan
ruwan lalle cokali daya don wankin dattin ciki
amma banda masu ciki, to yanzu dai zamu dauki
bangare daya daga cikin amfanin lalle muyi
magana akai, wato shine amfanin lalle da kuma
yanda ake amfani da shi don gyaran Fata.
.
.
Lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen
gyara fata ba, domin shi natural toner ne ba
bleaching yake ba amma yanasa haske mai kyau
kuma yana goge dattin fata, in kina son gyara
fuska tai kyalli, laushi da haske to ki kwaba lalle
da ruwan Kwai amma banda kwaiduwar kwan ki
kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci
shafa shi kullum minti talatin kafin wanka, za ki
sha mamaki in sha Allah:
.
.
Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da ruwa,
ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man
zaitun zakiga canji.
.
.
sannan gamai son kamshin fata
: Ki kwaba lalle da turaren ki mai kyau na ruwa
wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a
bucket ki sa garin lalle ya jika yay já zir sai ki
tsiyaye ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki
Bayan kinyi wankan sabulun ki sai ki dauraye
jikinki dashi inkin lizimci haka to bake ba rabo da
kamshin jiki in sha Allahu.
.
.
: Sannan ga gyaran duka jiki kuma zaki hada lalle
da sabulun salo da Zuma kina wanka dasu duk
zakiga canjin fata in sha Allah
Sannan ga Amare kuma
Kafin kiyi dilke na aurenki
: fata zatayi laushi, haske da kuma santsi.
Ki samu lalle mai kyau ki kwaba da turaren ki
mai maiko, turaren gargajiya mai mai dinnan to ki
jika kamar botiki ba ruwa ruwa sosai ba Kamar
dai kunu, kullum sai ki shafe jikinki da hadin
lallen nan duka jikin ki, sãi kizo ki saka turaren
wuta a kasko ko burner ki rufu akai ki turara
jikinki hayakin turaren nan ya shiga sosai sai ki
fita kije kiyi wankan ki zakiga canji.
.
.
Daga karshe kuma ga masu fama da pimples, sai
ki hada lemon tsami da lalle kwabi mai dan tauri
amma ba sosai ba kina shafa wa a fuskaar ki,
kuraje zasu mutu sannan tabo bazai zauna ba ga
hasken fuska da laushi.
.
.
Kuma lalle dai ba bleaching yake ba.
.
.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah.
.
whatsApp 08162600700

Post a Comment

0 Comments