GYARAN FUSKA>

<GYARAN FUSKA>

Asssalamu alaikum barka da warhaka

amare da dama suna fama da matsalar kurajen
fuska musamman farar mace Wanda sune sukafi
fuskantar wannan matsalar
Zanyi bayanin hanyoyi goma Wanda amarya
zatabi don magance matsalar kurajen fuska


(1) Da farko ana so awa biyu ko uku
kafin ki kwanta barci sai ki shafa man
goge baki a fuskarki, musamman
wuraren da kurajen pimples suke da
yawa. Ba kowane irin man goge baki
za ki shafa ba, ana so ki shafa farin
man goge baki ne. Idan kin ga dama
za ki iya wanke fuskarki idan man
goge bakin da kika shafa ya kai minti
30, idan kin ga dama kuma za ki iya
kwantawa da shi har zuwa wayewar
gari. Za ki rika maimata hakan har
zuwa wadansu kwanaki, idan kin yi
hakan za ki ga canji a fuskarki.


(2) Ki kasance mai yawan shan
ruwa.yawaita
shan ruwa ba wai zai sanya miki
laushin fata ba ne kawai, a’a, zai
taimaka miki wajen yaki da kurajen
pimples din da suke fuskarki. Haka
yana da kyau ki guji yawan cin
abincin gwangwani, kasancewar
suna dauke da wasu sinadarai da za
su rika sanya kurajen fuska. Ya
kamata ki yawaita cin ‘ya’yan
itatuwa da suka hada da su abarba
da lemu da ayaba da kankana da
sauransu.


(3) Ki rika amfani da abin shafawar
da ake kira ‘(Antiodident spray) irin su
(Jane Iradale) da (Neutrogenia Rapid Clear) da
(Acne Eliminating Spot Gel)
da sauransu, hakan zai taimaka miki
wajen daidaita man da ke fatarki,
wanda masana fata suka ce idan ya
yi yawa yakan haifar da kurajen
fuska.


(4) Ki kasance mai amfani da man
(Cornmeal) a fuskarki, yakan sanya
kurajen fuska su motse sannan a
hankali su bace, misali man shi ne,
(Intagilo Clear Sal Cleanser.) Sannan ki
rika amfani da man da ke hana
yaduwar kwayar cutar bakteriya, irin
wannan man yakan ratsa kofofin da
suke fatar fuskarki da ma jikinki gaba
daya, sannan yana yakar kwayoyin
cutar da suke fatarki, a lokaci guda
ya daidaita miki yawan man da yake
fitowa daga fatarki. Zai kuma cire
miki kwayoyin halittar da suka mutu
a cikin fatarki. Misalinsu; (Phytomer Gommage)
da Luffa-0.

(5) Yana da kyau ki ware wata rana
ko wadansu ranaku a cikin mako ba
tare da kin shafa kayan kwalliya a
fuskarki ba, hakan zai bai wa fatar
fuskarki samun ‘yancin shigar da
kuma fitar da iska ta kofofinta ba tare
da wani cikas ba. Haka idan za ki
shafa kayan kwalliyar a fuskarki, to ki
yi amfani da kayan kwalliyar da ba
sa toshe kofofin fatar fuska.

(6) Ki kasance mai shafa mai domin
fatar fuskarki ta kasance cikin danshi,
kasancewar wadansu kurajen fuskar
sun fi bata fuska idan fuska tana
bushe.

(7) Yi amfani da man (Tea Tree’)
domin ba wai kawai yana baje
kurajen fuska ba ne, a’a yana rage
karfinsu da kuma kalarsu. Za ki sami
ire-iren wadannan man a shagunan
sayar da kayan kwalliya na zamani.


(8) Ki kasance mai yin taka tsan-
tsan wajen amfani da ire-iren man
shafawar da kike amfani da su a
gashin kanki, ma’ana kada ki sake ya
rika taba fuskarki hakan zai iya haifar
miki da kurajen fuska, kasancewar
wadansu sinadaran an yi su don su
taimaka wa gashin kai ne, don haka
idan suka shiga kofofin fatar fuskarki,
sai su haifar miki da matsala.

(9) Ki kasance mai gasa kurajen
fuskarki: Duk lokacin da kurajen
pimples suka fito miki sai ki samu
wani kyalle mai tsafta, sai ki tsoma
shi a ruwan zafi, ba wanda ya tafasa
ba, bayan kin tsoma sai ki fito da shi,
sai ki rika dora shi a kan wajen da
kurajen suke, sannan ki rika gogawa
a hankali, zafin kyallen yakan sa
kurajen su motse daga nan su mutu.


(10) Ki guje yin amfani da hannunki
wajen fasa kurajen da suke fuskarki,
domin hakan yana kara yawansu
hade da sanya fuskarki ta kara
cabewa

Post a Comment

0 Comments