FARRAH EPISODE 3️⃣

 💫 FARRAH 💫








       ✍🏻M Shakur




EPISODE 3️⃣

Fizge hannunshi yayi daga hannun Baban nashi yawuce ciki yana tafiya kaman bayaso yayi agadarance Papa yajuya yabishi da kallo kaman baitaba ganin shi aduniya ba. “Yaya” Uncle yakirashi anatse dayasa firgigit yajuyo dasauri yana murmushi yace “kaga yanda Zayn ke kara girma kullum yamafini tsayi fa” dan murmushi Uncle yayi yace “ai tun Zayn na yaro yakeda saurin girma, babu wanda zai ganshi yanzu yabashi asalin shekarun shi 26 saidai adinga bashi 30 sama” sosai Papa yashiga dariya irinta manya yana kara leken Zayn din daya bace musu daga gani, sanan yajuyo yakalli Uncle yace “dan kanina ya akayi”? Yay maganan yana kama hannunshi cikeda so, murmushi Uncle yayi yace “zan wuce gida naje nai wanka nadan kwanta Yaya” cikeda so dakuma damuwa Papa yakai hannunshi kan shoulder nashi yace “you must be extremely tired ai dole ne, stress na Zayn is energy draining, kaje kai wanka kahuta I will see u anjima da daddare kokuma dasafe just take your time kaji idan zakazo ka taho da su Rukayya da yaran suzo su gaida da dan uwansu” gyadamai kai yayi ahankali yana murmushi yace “to Yaya bari naje” gyadamai kai Papa yayi yana sakinshi yace “u can dismiss wayan nan guards suma suje suhuta I will see you later okay” yay maganan Papa yawuce ciki.



Wani gagaruman falo Zayn yashiga yana tafiya kaman bayaso yayi ma’aikatan gidan tundaga nan compound ke zubewa suna gaidashi kaman anga Sarki ko kallonsu bayayi yashige falon abinshi, wata babban mata gatanan fara fat ke tsaye agaban dinning, tana sanye da wani arnen lace dayasha aiki mai suna aiki, idanunta sanye da fararen glasses kar wanda kana ganinsu kasan na kara karfin idanu ne, tana tsaye inda take tanama yan aikin pointing komi da yatsunta dasuka sha jan lalle tana nunamus yanda zasu jera abinci dakenan cikin lafiyayyun kuloli ubansu dakake gani a irin gidajen sarakunan larabawa tabama kofan baya hakan yasa ko kadan bataji shigowan Zayn dinba, kotaji ajikinta ana kallonta ne chak ta tsayar da maganan datakeyi da ma’aikatan sanan ahankali tajuyo kaman wanda wani abu yakirata, chak ta tsaya tana kallon Zayn dashima kallonta yake yana dan murmushi, ance uwa uwace kuma koyaya take dadi ne da ita, ahankali takai hannuwanta ta rungume su a kirji tai jim tana kallonshi daga sama zuwa kasa kaman mai tunanin wani abu tama kasa koda motsi daga inda take tsaye, wani kalan murmushi Zayn yayi dan yasan metake kallo sanan yataho da sauri har zuwa gaban dinning din ya tsaya agabanta yana kallonta yana murmushi ganin yanda tayi yasan fada zatamai hakan yasa kawai yakai hannuwanshi yajawo hannunta dagudu, ware ido tayi tace “mehaka Zayn? Mehaka kake jana”? Saida suka kawo tsakiyan falon sanan ya tsaya yakama dayan hannunta yarike yafara juyata yace “we are dancing Ummi, Ummi I am now taller than you sosai” yanda yashiga juyata yasa idanunta suka fara kadawa dasauri ta fizge kanta tana tangan tangan ta dafa kanta tace “jama’a na shiga uku, sabida kahadiyi kadan jimina kafini tsayi yanzu shine yabaka right kamin juwa juwa” dasauri tazauna akan kujera tana maida ijiyan zuciya, dariya yayi sosai yana kallonta kaman bashine ke kumbure kumbure awaje ba yazo kan kujeran datake yawani kwanta yadaura kanshi kan cinyanta sanan yakama hannuwanta yakai kan fuskanshi yana sauke ijiyan zuciya yace “massage my face Ummi nagaji” yay maganan yana lumshe idanu ahankali tafara massaging face nashi tana kallon gemunshi dayama kala sanan anatse takai hannunta kan gemun takama tarike tana kara tabbatar da kala ne wato tura gemun yayi murya chan kasa tace “Zayn wanan kalan dakama gemunka na menene”? Dan yatsine fuska yayi batare daya bude idanunshi ba yace “Ummi is fashion, bakiga Kenye west ba haka nashi yake” dan jim Ummi tayi sanan tace “Zayn menene abin burgewa anan amatsayinka na dan musulmi, annabi yace duk wanda yaso wasu kokuma yayi koyi dasu to ranan tashin alkiyama tare Za’a tashesu yana cikinsu, waye kuma Kanye west? Zayn haka mukai dakai? Bakamin alkawari zaka dawo yaro mai tsoron Allah ba dakuma koyi da sunnar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi, yanzu when was the last time kadauki Al Qur’ani ka karanta”? Minshari yawani jaaa irin baimasan tanayi ba dinnan kuma tasan sarai yana jinta, ahankali tace “Zayn ina maka magana kana minshar…..” “Why on earth are you disturbing my son Doctor? Daga dawowan shi” sukaji muryan Papa daya shigo dakin afusace hakan yasa tadago kanta dasauri takalli Papa zatai magana yadaga mata hannu alamun tai shiru yakalli Zayn din daya lumshe idanu yace “yaci abinci”? Girgixamai kai Ummi tayi, sosai fa cikeda masifa Papa yace “akan wani dalili zaki tasamin d’a agaba kina damunshi batare dakin ma bashi abinci yaci ba eh Doctor? Kinsan awa nawa yayi cikin jirgi nifa idan bakison yaron nan ni inason d’ana, nakuma san darajan shi, nasan me Zayn yamin, yaron nan yazame mini sila na farin ciki dakuma karin yalwan arziki dan haka kisan yanda zaki dingama d’ana magana, kome yakeso kibarshi yayi yaro ne he’s just 26, nan gaba koda kudi, bama kudi ba kodame zaki hadashi kice yayi shiga haka ko dressing haka wlh bazai yiba komi dakike gani na duniyan nan lokaci ne, Zayn” yakaraso wajen yana bambami yadago kanshi daga jikin Ummin dake kallon Alhaji turus kawai kana ganinta kasan batada tacewa, ahankali Zayn yatashi zaune yana dan bude idanunshi yana kallon Alhaji, dasauri Alhaji ya tallabi fuskanshi yace “kyale Maman ka tacika fitina, ni nasan sabida itane yasa bakasan dawowa Nigeria dan tasamin kai agaba take, yanzu ko zan tsaya tsakin daka babu wacce ta isa tadameka wlh, muje





Muje tabamu abinci kaci, tashi yayi kaman munafuki yabi Papa sukai dinning itakuma Ummi tabisu da kallo baki bude mamakin Alhaji take ba kadan ba, indai kan Zayn ne yiyakeyi kaman wanda akamai asiri, kullum kallon jariri yakema Zayn idan bai bari an tsawatamai yanzu ba yaushe za’ayi. “Zaki bamu abincin Doctor ko muyi serving kanmu”? Alhaji yay maganan rai abace, dan murmushi kadan Ummi tayi sanan tamike tsaye ahankali takaraso wajen dinning din sanan ta zuzzuba musu abincin white rice da fish sauce tun Zayn nakarami yanason abinci, ture nashi Papa yayi zuwa gefe sanan yajawo na Zayn gabanshi yana daukan cokali yace “yauwa lemme feed dan yaro na” tabe baki Ummi tayi idan da sabo tasaba da irin halayen nan na Alhaji, zama tayi anata kujeran ta debi abincinta tafaraci tana satan kallon Zayn din dake yanda yaga dama kafin yaci abincin da Baban nashi ke bashi, kaganshi zaka rantse he’s 10yrs old ne sabida yanda yakeyi, dan girgiza kai kawai tayi aranta tace “Allah ya shirya” Zayn yalalace na karshe mahaifinshi yaki bata daman ta gyara yaron nan tun kafin yakawo haka amman yanzu kam saidai suyi duk fadan dazasuyi zata sakama danta idanu, bude kofan falonsu akayi aka shigo da sallama wasu manyan mata ne su uku gasunan kaman Ummi suma sunci gayu na alfarma suna washe baki,  wacce kea gaba ne tace “yau danmu yadawo Zayn andawo laf…..” hannu Alhaji yadaga musu sanan yanuna musu kujerun dake falo yace “ku zauna kujirashi yagama cin abinci sanan ya amsa gaisuwan ku kada kusa ya kware abinci yakeci” yana maganan yajuyo yana kai abinci bakin Zayn din dako nuna alamu baiyiba na yaji matan Babanshi sunzo ana gaidasu ba, Ummi jitayi kaman ta kurma ihu Wanan wani irin wulakanci ne, ko ita akama haka bazata ji dadi ba an shigo da murna Ama danka sannu da zuwa kamusu Wanan wulakancin saikace beggars, ture abincin gabanta tayi tamike tsaye tana kakalo murmushi tana kallonsu sanan tataho falon cikeda mutunci tace “Hajiya Hadiza, Hajiya Fatima, Hajiya Maryam sannun ku da shigowa, bismillan ku kuzo muci abinci please” wacce tafisu kiba duka Hajiya Hadiza ne tai dan yake tace “ahh Alhamdulilah akoshe muke, Sarki mukazo gaidawa daman akace mujira yagama cin abinci” dan murmushi Ummi takara yi sam bataji dadin maganan da Alhaji yagaya musu ba, ahankali ta nemi kujera one sitter ta zauna sanan takalli karaman cikinsu wacce itace amaryan Alhaji bazawara ce ya aureta kusan sa’an Ummi nema ahankali tace “Hajiya Maryam ya zaman kadaici” murmushi tamata dudda yanzu shekarunta biyu da aure amman kowa referring nata Amarya yake duk cikinsu itace mai dan shiri da Ummi, cikeda fara’a tace “lafiya kalau Ummi, Ya patient kuma? Yaushe ne tafiyan dazakiyi na UNICEF”? Dan ajiyan zuciya tayi tace “wlh da badadan aikin taimakon al Umma bane, taimakawa marasa lafiya da magunguna na karkara haka da tuni nafice daga team din UNICEF na Nigeria, aikin nada wahala team dina zamuje kauyuka daban daban guda 10, in 3days time ne tafiyan Allah dai yabamu sa’a” Hajiya Maryam tace “Ameen, Allah ya taimaka” cigaba da hira sukayi dukansu sama sama.



Tass yacinye abincin da Alhaji kebashi abaki dan Zayn nadacin abinci sosai ko maybe saisa ma yakeda tsayi oho, tissue Alhaji yasa ya gogemai baki tass sanan ahankali kaman zaiyi magana da jariri yace “ga step Moms dinka sunzo jeku gaisa” wani irin yatsine fuska yama Alhaji ashagwabe kaman baiso yay magana yace “I am tired Papa, I want to sleep, I can’t see them now” gyadamai kai dasauri Alhaji yayi yana shafa fuskanshi yace “to to shikenan, tashi muje kayi baccin ka” Alhaji yamike dasauri yana kama hannunshi zai dagashi, tashi tsaye yayi ahankali duk aka bisu da kallo suka taho falon babu wacce ta isheshi kallo cikinsu, Alhaji dake taredashi yakallesu yace “bacci Zayn yakeji yanzu, yagaji anjima kudawo ku gaidashi idan yatashi daga baccin” yay maganan yana kama hannunshi zasu fice daga dakin, Ummi jitayi ranta ya bala’in sosu no this is the limit dazata dauki iskancin Zayn, budemai kofa Alhaji yayi zai fita cikin kakkausan murya Ummi tace “Zayn!” Chak ya tsaya batare daya juyoba, cikeda fada Alhaji yakalleta yace “wai mekuma baraki barmin yaro yahuta ba”? Cikeda bacin rai Ummi tace “Alhaji enough please! Ba gata kake ma yaron nan ba wlh, iyayenshi ne nan zaune sun taso tundaga various bangare nasu sunzo nan dan sugaida Zayn wanda bahaka yakamata ba ai shine dansu shiya kamata yaje one after the other ya gaidasu iyayenshi ne, yanzu kuma sunzo sun gama jiranshi yace yagaji bacci yakeji su dawo anjima sabida zamanshi suke wani irin rashin da’a da tarbi……” Kul! Alhaji yafadi cikeda bacin rai yana nuna Ummi da yatsa yace “kada kisake ki kira yaro na mara tarbiya kafin kija bakinki yabishi, idan bakison yaron nan ne kigayamin zan daukomai the best Nany in this entire world dazata dinga kulamin dashi, inda ma na iya girki kin zaci zan bari d’ana yadingacin abincin wasu ne konaki ma? Jarabanki, masifanki, korafinki da damuwanki yasa Zayn bayason zaman gidan nan bayason dawowa Nigeria sabida kin tasashi agaba yi wanan bar wanan haba, kinsan irin wahalan danasha kafin nasamu ya yarda yadawo Nigeria, kinsan awa nawa yayi cikin jirgi yanzun nan yadawo yaci abinci yagaji yanajin bacci nace sudawo anjima su gaidashi barasu dawo bane! Akwai wanda ya isa yajadani cikinku ne, dukanku nan zaman mahaifinshi kuke, nace anjima adawo agaida Zayn akwai wanda ya isa yajadahakan ne!” Yabuga uban ihu dasauri Hajiya Hadiza tamike tana yake cikin makirci tace “Ahhh abu yay zafi Alhaji kamata hakuri, babu wanda ya isa yaja dakai, zaman ka mukeyi wlh! kasan Shafa’atu har yanzu yarinya ce, wani zubin gidan dakataso ma yana affecting mutum, kaga muda muka taso gidan masu shi munsan yanda akeji da yara, yaran mu sune number one kome sukeso yazauna, yan gidan talakawa dama haka suke sai hakuri, basusan menene ririta danda suka haifaba saidai su wulakanta shi, bama su iya son yaransu ba sabida basu taso cikin gata ba, Zayn yaje yay bacci abinshi anjima ma dawo, Zayn Son sorry kaji anata bata maka rai daga zuwanka, uwarka sai ahankali, Alhaji ayakuri dan Allah” yanda Alhaji yaji dadin magananta ko baisan lokacin daya tura hannunshi a aljihunshi yaciro key wata Babban jeep nashi that worth 70M yajefa mata yace “nabaki motata Hadiza” wani irin ihu tayi tazube akasa shikuma Alhaji yakama hannun Zayn dayadan saci kallon Ummi datai jugum azaune tana kallonshi suka wuce suka fita zuwa bangaren shi.






Tashi Hajiya Fatima tayi cikeda bakinciki da kishin Hajiya Hadiza tafice fuuu daga dakin, sanan itakuma Hajiya Maryam ta tashi tana dan kakalo murmushi tace “akashe lpy Hajiya Hadiza” sanan takalli Ummi tace “sai anjima Hajiya” Gyadamata kai kawai Ummi tayi takasa magana, saida tagama dariyanta Tsaf sanan tamike tsaye takalli Ummi daga sama har kasa tace “ohh’uhh ni wlh har tausayi kike bani dan banga banbancinki da mu dabamu haihunma Alhaji ba, da wanan haihuwa ai gwara bakayiba, yaro bayajin maganan ki baki isa dashi ba, baki isa ki tofa wani zance kanshi ba ubanshi ya hayayyako miki kina bani tausayi Ummi” tawani kwashe da dariya tana juya key motan hannunta tace “jibi kyautan motan dana samu Allahu Akbar” takara kecewa da dariya sanan takalleta tace “dan da ake mana gadara dashi ana daddaga mana kafada kalleshi, da inhaifi d’a dai irin danki Ummi gwara na mutu bantaba haihuwa ba, wai inata cewa danki, dan mijinki” tasake kecewa da dariya sanan tawuce tafita daga dakin tai waje Ummi jitayi hawaye sun saukomata daga idanu sharrrrr dasauri tasa hannu ta share, duk gidan nan kap itace tafito daga gidan talakawa, bayan tagama secondary school taci scholarship da Alhaji ke bayarwa every year taje takaranci medicine gynecology, ranan da tai graduating a ranan ne tafara ganin Alhaji sabida angayaceshi yazo yaga graduation na yaran dayabama scholarship kuma a ranan yaga Ummi yaji yanaso itace matarshi tabiyu, Hadiza ce babba sai ita sai Fatima sai Maryam ta karshe

.

Post a Comment

0 Comments