_🕊️SABON TAKU!🕊️_
_(Ƙwarton manya return)_
Free page
002
*AUNTY AISHA MMN TEDDY*
_Ba zanyi free page da yawa ba , free page zai ƙare nan kusa hanzarta wajen mallakar taki... Regular payment₦300 vip group₦500 special₦1000...Zaki iya turo da katin MTN ta wannan number 08081202932 ko ki tura kai tsaye ta wannan account details...6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,sannan ki tura shaidar biyanki ta wannan number Nawa 08081202932_
Masu tambayar complete na SABON TAKU! ba complete Yanxu ake typing 🙏
***
Kallon su Sha'awanatu keyi tana jin wani irin ɗaci da huci a zuciyar ta. Jin ta take kaman ta shaƙo wuyar su Fu'ad ta huta saboda haushi da takaici. Maganan tasa ce ta nanata da yake faɗin Sha'awa! Sha'awanatu sha'awar ki nake...tirrrr Allah yayi mana tsari Haushin kan ta tafara ji da yanda ta tsaya tsawon shekaru tana biye mawa su ƙwazin ɗin nasu... Inalallahi wai'ina ilaihir rajiun shine kalmar da sukaji yana karaɗe ciki da wajen ko ina na gidan...Muryar Su Ammie da sauran matan gidan ne wato iyayen su ya sa su saurin dakatawa daga duk wani abu da suke na lalata. Da gudu Sha'awanatu ta fiche yayi da Su Fu'ad da sauran samarin gidan fitowa cikin sauri cike da kiɗemewa,don basu taɓa jin sallallamin iyayen nasu haka ba.
Abun ko da ya faru shine bayan fitar su Ammie ,su Hadiza ana can ana ta addu'ar Allah ya sauke Mufeeda lafiya ,wanda cikin Allah da ikon shi ,Allah buwayi gagara misali , Mufeeda ta sauka lafiya ta haifo lafiyayyar ɗan ta namiji cikakken ɗan wata tara. Naɗe shi da Towel Ammie suka yi ,yayin da Mama Rabi ta nufi toilet don haɗa mata ruwan ɗumi ,ita kuma Ammie ta nufi Part ɗin ta don ɗauko su bagaruwa da sauran kayan da zai haɗa mace . Wannan daman Mufeeda ta samu tana waigawa taga ba kowa a Bedroom ɗin da take , wannan yasata sumfutar yaron tana fichewa daga Part din da gudu... farfajiyar gidan ta nufa tare da Nufar bayan gidan ,inda suke kirar wurin da Back yard. Tsohuwar rijiya ce wanda tun da suka taso a rufe suka ganta babu wanda ya taɓa ganin an buɗe ta ,don zurfin ta ,tare da wasu irin injina dake ciki , koda za'a yi haƙar rijiyar ɗauko turawa iyayen nasu sukayi na musamman akayi wannan zuzzurfan rijiyar . Wanda ganin irin haɗarukan dake ciki yasa Su Abba sakawa aka rufe shi tuni ,da yawa Basu san ya rijiyar take ba ciki harda ita kan ta Mufeeda da ta nufi rijiyar tana ɗaga murfin ta ,wanda shi kan shi ɗagawa jidali ne....ji kake tumjummmmm sai kaji ƙiiiiiiiiiii na urorin dake rijiyar sun ɗauki ƙara wanda wannan shi yasa ka duk wani wanda yake numfashi a cikin gidan nan jin wannan sabon Al'amarin da basu taɓa jin irin ta ba. Su Ammie suka fara fitowa harda Umman Ƴaƴa ye ,wato kakar su. Wurin ma'aikatan gidan da securities suka nufa da gudu ....wanda anan suka yi arba da Mufeeda tana cillar da Towel ɗin da Ammie ta naɗe jaririn dashi ... Mufeeda saka yaron kikayi a rijiya??? Mama Rabi ke maganan cike da Rawar murya ...wanda cikin wani irin yanayi na rashin nadama Mufeeda tace " Eh Mama Rabi na huta ,shima ya huta.. inalallahi wai'ina ilaihir rajiun a tare su duka suka ambata yayin da Ammie ke faɗin mun shiga uku...Yah ilahi ya Allah! Tsoro ne ya kama Fatima don ita haka take ga tsoro ga tsiwa ,tsiya kam babu wanda yakaita da hayagaga. Amma ganin irin abun da Mufeeda tayi nan take ta tsaga ihu tana yanke jiki tare da yin baya zata faɗi su Hadizaa sukayi saurin tare ta ....
To kunga ɓarnan da kuke yi kenan a cikin gidan nan, inalallahi wai'ina ilaihir rajiun ,wannan wani irin rayuwa ce? Wasu irin ƴaƴa muka haifa? Fu'ad Shamsu da kuma duka , wallahi na gaji da wannan halin naku ,kun isa munzali don haka kowanne ku duk wani ɗanamiji dake cikin wannan gida , na bashi daga yau zuwa gobe kowa yayi takan shi ...kuje kuyi na ku gidajen sai ku cigaba da iskancin ku a duniya....yah Isa haka Ammien Maleek abun yayi yawa? Mene jikoki na sukayi ? Babu inda zasu tafi .nan gidan iyayen su ne ,basu da inda yafi nan....kina nufin Harda Maleek ɗan shekara ashirin da biyu shima ya bar gidan to babu wanda ya isa ko su iyayen nasu maza zasu zo basu isa ba....kuma wannan abun da suke ai bakomai ba ne...lafiya ce dasu , sun isa ne ,sun kai munzali da misali. Umman Ƴaƴa ye ke maganan tana haki kaman tare da faɗa Ammie Maleek da faɗa.
Mama Rabi ne cike da jin zafin goyon bayan da Umman Ƴaƴa ye keyi akan jikokin ta ta kauda kai tana watsa mawa su Fu'ad wani mugun Kallo , kamin tace " Ku ɓace ku bamu wuri...don baku da amfani ba abun da kuka iya kuka sani sai ƙwartanci. Malam Garba taimaka ka kira su Alh Bashir su san halin da ake ciki don babu bil'adaman da zai faɗa rijiyar nan asa masa ran rayuwa. Kamin ta rufe baki Umman ƴaƴaye ne tace " Allah ya kiyaye na gaba. Kai ku mu wuce kowa yaje yayi sha'anin sa...tayi maganan tana kallon jikokin nata da kowa ya fara shirin barin wurin jiki babu ƙwari.
Dafe kai Ammie tayi tana girgiza kai , tare da kallon yaran da zamuce gomma matan sun nuna jimami mazan kuwa ko a jikin su. Wani irin matsiyacin horn suka ji , wanda dagaji sun san me irin wannan horn...cikin sauri ma'aikatan kowa ya fara warsewa ,wasu har da gudu. Masu gadi suna nufar gate ɗin cikin sauri , don sun san waye Maleek shi ko inuwa bai son yagani na talaka! Janye Gate ɗin suka yi da sauri ,wanda kaman yana tsakiyar ƙwalta haka ya shigo farfajiyar gidan cikin wani irin gudu bai damu yabi takan koma waye ba.
Mareeya ce ta iso inda moton nashi yake da gudu tana buɗe murfin moton kamin yayi magana sai ga sauran yayyun nashi mata da maza duk sun zagaye shi suna tambayar Ya wasan Damben nasa? Suna fatan dai shi yayi nasara a wannan karon! Kallon su yayi tare da kallon hannun shi ,wanda wasa na uku kenan duk idan yazo za'a fara wasan hannun sa ke ƙamewa lamƙwasa ta baya iyayi bare yayi wani abu wai shi dambe! Idon sa ne ya sauya yayi jahhh gasu a ƙaƙkafe na rashin kunya da tijara . Yah Mareeya na bar dambe har Abada!
Maleek! Suka haɗa baki suna kirar shi a lokaci ɗaya.
Wanda Ammie kallon su tayi tana jin wani irin abu ya tokare mata a wuya...ganin yanda sunyi kisan kai a cikin gidan ,amma kaman ba mutum aka kashe ba...tambayar ƙwallo ma suke .. ina Mufeeda! Suka ji Muryar sa ya katse su ba tare da ya damu da razana da furucin sa ba. Kallon sa sukayi Hadiza ne tace " Maleek kabar damben to yanzu me zaka koma?. Bai bata amsa ba , ya ɗaga kansa yana hango Mufeeda dake share hawaye....shiru yayi yana ɗan nazari wanda a hankali ta tako inda yake , Yah Mufeeda kin haihu ne???. Murmushi tayi tana jin yanxu take saƙatttt ta huta da duk wani musiba da ta jawo mawa kan ta....bata basa amsa ba sai cewa tayi " Ƙanina idan ka daina dambe to me zaka koma yi kenan! Tayi maganan tana kallon yanda komai nasa yake a murmuɗe irin na mijiya ƙarfin mazan nan ,wato ingarman namiji. Ga tsawo ga zati bakyace shine ƙaramin su ba. A hankali ya motsa laɓɓan sa yana cewa " SOJA!
_#SHERE MASOYA MUTANEN AMANA_
*Littafin Sabon Taku na kuɗi ne normal group ₦300 vip group₦500 SPC₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ki tura katin MTN ta wannan Numbobi 08081202932*
*ROYAL GELLY* *(MAIDA TSOHUWA YARINYA)*
🔥🔥🔥💃💃💃💃
Wani kayan sai amale wannan supplement shi akecema maida tsohuwa yarinya ita Kuma yarinya ta koma jaririya😂💃💃💃
Ina kuke Mata masu aji waanda sukeso suga suna walwali kamar tauraro toh gafa dama tasamu kiyi washar washar abinki.....🔥
⭐ Royal jelly nasa jikin mace yayi glowing mace jikinta yayi Kamar tangaram😍.
⭐Royal jelly natsoro da gashin mace yayi kyau...
⭐Royal jelly na gyara mace ciki da wajenta..
⭐royal jelly na fidda shape din mace...💃💃
⭐ Royal jelly na Hana fatar mace tamukewa , yasa tayi looking fresh ...
⭐Yanasa mace yayi looking under age dinta💃💃kiji ana wacce ke kullun kamar wata budurwa🔥
⭐ Royal jelly nakara hasken Ido yakuma gyara gashin ido 🔥
⭐ Royal jelly na tsirar da farce da kwarinshi...
Idan kinji ana maganar glowing to kici birki a royal jelly na masu buƙata ku tuntuɓi wannan Numbobi 08081202932 / 09061466409🔥🔥👑👑💃💃
*AUNTY MMN TEDDY*
0 Comments