iRashyder
ADO DA KWALLIYA
GYARAN GASHI
Kafin ki fara gyaran gashi akwai buqatar sanin
kalan gashin ki ina nufin type dinsa ba wai fari ne
ko baqi ba
DRY HAIR
Zaki ganshi ko da yaushe a bushe daga kin shafa
mai nan da kwana daya ya bushe fatar kanki fari
tas sometimes yana sa dandruff mai gari idan
rashin kulawar tayi yawa sanna gashin baya
tsawo yana saurin kakkaryewa. Wannan gashin
yafi kowane buqatar gwata sai kinyi da gaske in
har ba sou kike ki zama kwakwido ba at least
koda gashin bazai karu ba dai tou ba'a so ya
ragu
OILY HAIR
Zaki ganshi ko da yaushe cikin maiqo sannan
yana saurin jiqewa idan kin shiga rana irin
wannan gashin wari yake yi idan ba'a yawan kula
dashi especially idan akwai amosari ko kuraje
akan... Domin idan ciwo ya shiga cikin gashin
nan ruwa yake yi wanda hakan ke sanya wa
gashin wari
NORMAL HAIR
Wannan bashi da wani matsala zaki ganshi ba a
bushe ba kuma ba'a jiqe ba yana da kyau sosai
very fresh
COMBINATION HAIR
Wannan gashin yawanci zaki same sana qasan
(wato daga keyan ki xua kasa) yana da maiqo ta
saman kuma abushe ko kuma normal shima
wannan gawhin sosai yake buqatar gyara.
SENSITIVE HAIR
Wannan gashin bashi da kyau sam... Kuma rashin
gyara ne yake kawo shi tare da too much iyayi
komai kika samo ki laftawa gashin ki sai yazo ya
lalace kullum yay ta karyewa ga yawan kuraje da
amosari wani lokacin ma gashin zai zama dai dai
dai dai kamar dai mutum ya zauna ya irgasu.
Hakan yana faruwa a kowame launin relaxer na
lissafa a sama.
Wadannan suna kalolin gashin da muke dasu
gaba daya wanda akwai hanyoyi da yawa da zaki
gane irin su gareki da kuma yanda zaki magance
sa cikin sauki amma fa zai dauki lokaci sannan
kafin ki fara akwai buqatar ki san wannan
BANBANCIN SHAMPOO DA RELAXER
Mutane da yawa sun san banbancin su kazalika
mutane da yawa basu sani ba dan haka akwai
buqatar ayi masu uzuri.
SHAMPOO kamar sabulu ne na ruwa wanda ake
wanke kai da shi baya qara komai baya rage
komai sai dai idan anyi shi mussamman dan yayi
din. Wanda idan hakan ya kasance zaki ga an
rubta a jiki.
RELAXER wannan kuma wani mai ne mussaman
da aka kirkire sa don gyaran kai musamman ga
baqaqen fata mai gashi a cushe idan suna
buqatar gashin su ta kwanta tayi kyau kamar na
fararen fata sai suyi amfani da ita.
NATURAL HAIR
Idan akace natural hair ana nufun wadanda basa
sa relaxer (famin ko kumfar los.. Mama jugu jugu
da sauran su). Sabida rashin lokaci yau zanyi
bayanin yadda mai natural hair zata kula da
gashin ta idan Allah ya kaimu next week sai muyi
na masu sanya relaxer.
Da farko dai shin gashin mu na baqaqen Africa
gashi ne wanda yafi na ko wane ginsi kyau
lisabab... yana buqatar gyara sosai sabda
adunkule yake wanda hakan ke hana asalin
maiqon dake fatar kanki (natural sebum) wazuwa
har bakin gashin ki rashin faruwan hakan kuma
yana taimakawa wajen kakkarye gashin wato
sabo na fitowa tsoho na karyewa.
SHAMPOO
Zai dace ki bar amfani da ko wane irin shampoo
musamman wandanda suke dauke da sinadarin
SULFUR.. PETROLEUM DA SODIUM domin suna
dauke da sinadarin busarwa irim wanda ake
amfani da su a sabulan wanki omo da sauransu
don haka duk lokacin da zaki saya sai ki duba
ingredients din idan kuma yq zama dole sai kinyi
amfani dashi tou sai ki surka shi da ruwa daidai
adadin sa. 50-50 kenan ko kuma ki nemi MILD
SHAMPOO wannan bashi da chemicals masu zafi
sosai. Amma organics is the best option
ORGANICS
abun da ake nufi da organic shine natural abu
wanda ba'a yi amfani da wani harsh chemicals
(kemikal masu qarfi) wurin sarrafa su ba kamar
dai wasu nau'ika da nau'in abinci da ake
sarrafawa acire wani abu daga cikin sa
Yafi dacewa abun da ya kama daga man
shampoo conditioner man kitso da duk wani abun
da zakiyi amfani dashi a kanki ya zama natural
ko kuma organic Domin duk man da kika shafa a
fatan kanki yana shanyewa sannan jini ya tafi
dashi zuwa hantar ki daga nan kuma ya cigaba
da wanzuwa ko ta ko ina don haka yake da
matuqar mahimmanci kisan irin abubuan da zaki
na sawa a kanki saboda tsaro.
CONDITIONER
Shi conditioner ana amfani dashi ne dan a dawo
da taushin da aka rasa na gashi. Yanda ake
amfani dashi kuwa shine bayan kin gama
shampoo kin dauraye tas! Sai ki shafa
conditioner tun daga qasan gashinki zuwa bakin
sannan ki samu leda ki rufe gashinki ki daura
dankwali ki barshi na tsawon lokacin da suka
rubta a roban. Bayan nan sai ki wanke ki
tabbatar baki barko kadan a cikin gashin ki ba
don kar yayi maki illa.
Amma sau daya ake yin hakan a wata daga nan
du ranar da zaki wanke kanki baza ki sha shi a
fatar kanki ba gashin kawai musamman karshen
gashin (ina nufi. Inda kike kamawa da ribon)
Ga wadanda suke wanke gashim su kusan kullum
yana da kyau ya kasance duk lokacin da zaki sa
ruwa a kanki to kiyi amfani da conditioner ki
dauraye hakan zai sa gashin yayi maintaining
moisture dinsa sannan idan ya bushe sai kiyi
oiling (oiling yana nufin shafa mai lungu da saqo)
COMB
ki riqa amfani da qaton kum mai manyan haqora
ko kina da gashi ko baki dashi domin karamin
kumb yana tuge gashi
Sannan ki sayi daya safaya ki ajiye wajen sa da
ban saboda baki idan ba haka ba kullum aikin ki
baya xai riqa dawowa duk wani abun fa kike
amfani dashi a gashi ya zama naki ke kadai ko
ke da yaran ki. (Idan kina kula da gashin kansu
kenan)
OILING
Yanda zaki fiqa shafa mai akan ki shine ki riqa
sagawa kanana kina shafa mai daga fatar kanki
zuwa qarshen gashin har ki gama sannan ki
zauna kiyi ta massaging gashin kamar kina susa
kaikayi amma a hankali dan man ya natsu a ciki
idan na tsawon minti 30 ko awa daya ma idan
kin gama ki tace sannan ki qara shafawa bakin
gashin mai sosai.
Rashin shafa mai a bakin gashi shi yake kawo
karyewan gashi sabo na fitowa tsoho na karyewa
gashi baxai taba yin tsawo ba kenan.
PROTIEN TREATMENT
Yana da kyau ko wani wata ki riqawanke kanki
da kwai misali bayan kin wanke kai kin tsane
ruwan tas ya fara alaman bushewa sai ki fasa
kwai wasu suna amfani da farin ne kawai wasu
kwaiduwan (york) wasu kuma both duk dai wqnda
kika zaba sai ki shafa bayan awa daya ki wanke
ki dauraye da conditioner zai sa gashinki shining
(kyalli) da kyau . zaki iya hada kwan da ayaba da
madara wannan ma yana da kyau sosai ya kuma
qara bakin
Gashi. Amma fa kar kiga ya qarbe ki kije kiyi tayi
toh ba ruwana idan ya kakkabe gashin..... Sau
daya tak! A wata
SALOON
Ki dainq yawan zua saloon ana kona maki gashin
ki abanza yana karyewa gara kina gama wanke
kanki kiyi kalaba ki barshi yabushe washe gari ki
tsefe ki shafa masa mai
Idan kuma ya zama miki jiki amfani da kayan
wuta a gashi don warware gashi tou gara ki shiga
dryer (draya) yafi sauqi da rqwhin karya gashi
sannan kuma ki siya HEAT PROTECTION
SHAPOO, MOISTURIZER, SPRAY KO KUMA
SERUM ki fara sawa a gashinki kafin a fara
qonawa.
Ya kamata mu tsaya anan zan cigaba next week
insha Allah wslm.
AdoDaKwalliya
@arewashow
0 Comments