SHUGABANCIN MACE A MUSULUNCI

*_SHUGABANCIN MACE A MUSULUNCI_*
*Tambaya* Assalamu alaikum. Malam Don Allah
menene fatawar malamai magabata akan
shugabancin mata, kuma zan so ayi post mai
zaman kansa akan wannann matsala. Allah ya
taimaka. *Amsa* Wa'alaikum assalam Yawanci
malamai magabata suna tafiya ne akan hadisin
Abu-bakrah inda Annabi ﷺ yake
cewa; "Duk mutanen da suka sanya mace ta
zama shugabarsu, to ba za su rabauta ba"
kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi
mai lamba ta: 4425. Don haka bai halatta ta
rike shugabanci ba in ba na gidanta ba. Sannan
malamai sun ce daga cikin hikimomin hakan shi
ne: saboda raunin mace, da tawayar hankalinta,
da kuma yawan tausayinta, sannan idan tana
haila halayanta sukan canza, ka ga za ta iya
yiwa mutane danyen hukunci. Ibnu Khudama
yana cewa: "Annabi ﷺ bai taba
sanya wata mace a matsayin shugaba ba, haka
nan halifofinsa shiryayyu". Mugni 13\14. Duk
lokacin da mutane suka dorawa mace
shugabanci lamura za su tabarbare, kuma
hakan har lahirarsu sai ya shafa, Shaukani yana
cewa: "Babu wani narko da ya fi kore rabauta"
Sailul jarrar 4\273. Allah ne ma fi sani.
21/10/2014 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ. Ya kai dan uwa mai
Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako
zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi
yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta
bawa ga Mahalicci.
______________________________________ » Zauren
🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). Ga
ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a
whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa
ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.

Post a Comment

0 Comments