Amfanin Dabino (Date fruits)

AMFANIN DABINO (Date fruits)

***************
Dabino yana daya daga cikin
kayan itacen da Annabi (saww) ke so.

1. Yana saurin narkarda abinci
2. Yana Sanya kuzari yayin Ibadar Aure
3. Yana taimakawa wajen kara jini
4. Yana taimakawa Ma'aurata maza/mata
5. Yana Maganin Basir Mai sa tsugunni a bayi. 6.
Yana karawa Ido lafiya
7. Yana Rage Nauyin kiba da teba.
8. Yana Maganin Gudawa
9. Yana Saurin Saukarda Hawan jini
10. Yana taimakawa kwakwalwa wajen Samun
basira..
11. Yana kariya daga Sihiri
12. Yana taimakawa Mata masu ciki dan samun
sauqi wajen
haihuwa.
13. Yana kariya daga Sihiri.

**YADDA ZA'AYI
AMFANI DA DABINO.

CIWON NONO GA WACCEN DA TA
HAIHU;
Anacin dabino guda 7 asha man
tafarnuwa karamin cokali sau 1
arana kwana uku.

**DOMIN SAMUN NI'IMA GA MA'AURATA;
Ana daka dabino a zuba cikin madara (freesh
milk) sannan a saka Zuma a ciki a sha awa daya
kafin a kwanta. GA MATA MASU JUNA BIYU;
Ana cin dabino kwara bakwai kullum da safe idan
anyi kusan haihuwa Wannan yana hanawa
macce yawan zubar jini lokacin haihuwa da iznin
Allah.
**GUDAWA;
Ana daka garin dabino a saka a
ruwan zafi a sha In shaa Allahu
yana tsayar da gudawa.

**SAMUN KUZARI;
Ana cin dabino guda ukku a sha zuma cokali 1
da safe da yamma.

**SAMUN LAFIYAYYAR FATA;
Ana hada garin dabino da zuma da man zaitun a
shafa a fuska awa
daya sai a wanke fuskar da ruwan zafi wannan
yana saurin gyara fuska.

Bin cike ya nuna Yawaita cin dabino na hana
kamuwa da ciwon
CANCER ko wacce iri.
**Haka Kuma MANZON ALLAH (saww) YACE
DABINO AJWA YANA MAGANIN DUKKAN
CUTATTUKA, KUMA DUK RANAR DA
KACISHI,BABU WATA
CUTA DA ZATA SAMEKA AWANNAN RANA, KO
KUMA SAMMU KO SIHIRI.

Wasu MALUMMAN MUSULUNCI kuma sunce
Annabi (saww) Yana
nufin kowanne dabino ba wai sai
Ajwaba (Wallahu A'alam)

Post a Comment

0 Comments